Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-04 18:19:05    
Kafofin watsa labaru na Afrika sun nuna yabo sosai ga taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan harkokin hadin kan Sin da Afrika

cri
Ran 4 ga wata, an bude taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan harkokin hadin kai a tsakanin Sin da Afrika. A cikin kwanaki a jere, kafofin watsa labarum Afrika sun bayar da labaru daya bayan daya, inda suka mai da hankali da nuna yaro sosai ga wannan taron koli, suna ganin cewa, wannan taro zai zama wani taro mai abubuwa da yawa, da kuma ma'ana sosai, wajen tattauna babbar manufar raya kasa, da sa ran alheri ga makomar samu moriyar juna a tsakanin Afrika da Sin.

Jaridar "Cameroon Tribune" ta hukumar kasar Cameroon ta bayar da labari cewa, taron kolin ya ciyar da kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afrika zuwa wani sabon matsayi.

Jarida " The Zambiya" ta Zambiya ta ce, taron koli zai karfafa cudanyar da ke tsakanin Sin da Afrika a duk fannoni.

Jarida " Times Rthiopian Herald" ta kasar Habasha ta bayar da labari cewa, a cikin shekaru 6 da suka wuce, dandalin tattaunawa kan harkokin hadin kai a tsakanin Sin da Afrika ya ba da taimako sosai kan inganta kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afrika cikin dogon lokaci a duk fannoni, kuma zai tsara wani kyakkyawan fasali na nuna amincewa da juna wajen siyasa, da samu moriyar juna wajen tattalin arziki, da kuma yin cudanyar al'adu. (Bilkisu)