Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-04 18:17:17    
Mr. Hu Jintao ya gana da shugabannin kasashen Equatorial Guinea, da Mali, da kuma firayin ministan kasar Habasha

cri

Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya gana da Mr. Amadou Toumani Touer shugaban kasar Mali

Ran 4 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya gana da Mr. Obiang Nguema Mbasogo, takwaransa na kasar Equatorial Guinea, da Mr. Amadou Toumani Touer, takwaransa na kasar Mali, da kuma Mr. Meles Zenawi, firayin ministan kasar Habasha.

Da farko, Mr. Hu Jintao ya yi maraba da godiya ga shugabannin kasashen 3 sabo da suna halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan harkokin hadin kai a tsakanin Sin da Afrika.  Yana fata bangarorin biyu su dauki wannan taron koli na dandalin tattaunawa a kama da sabon masomi, za su yi kokari tare don kara ciyar da kyakkyawar dangantakar hadin kai da ke tsakanin Sin da Afrika gaba.

Shugabannin kasashen 3 sun nuna cewa, ya kasance da zumunci sosai, da moriya daya a tsakanin jama'ar Sin da Afrika, kira taron kolin, yana da ma'ana sosai wajen ingiza hadin kan Sin da Afrika, da kuma hadin kan kasashe masu tasowa. 

Bayan haka kuma, shugabannin kasashen uku sun bayyana cewa, akwai Sin daya tak a duniya, suna tsayawa kan manufar Sin daya tak.

A lokacin da shugaba Hu ya gana da Mr. Toure, shugaban kasar Mali, ya ce, gwamnatin kasar Sin ta darajanta zumuncin gargajiya da ke tsakanin Sin da Mali, tana fatan ingiza bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a duk fannoni.  Mr. Toure ya bayyana cewa, kasashen Mali da Sin sun hada kansu kamar yadda ya kamata a duk fannoni, kuma sun sami sakamako mai kyau.  (Bilkisu)