Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-04 12:04:45    
Sabunta: An fara taron koli na Beijing tsakanin Sin da kasashen Afirka

cri
A ran 4 ga wata da safe, an fara taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka. Shugaban kasar Sin da shugabannin kasashe ko gwamnatoci na kasashe 40 na Afirka sun halarci taron.

A gun bikin kaddamar da taron, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayar da jawabi, inda ya bayar da manufofi 8 domin ciyar da sabuwar alakar dangantakar abokantaka a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka gaba. Wadannan manufofi 8 su ne, da farko dai, kasar Sin za ta kara samar wa kasashen Afirka yawan kudin taimako, wato yawan kudin taimakon da kasashen Afirka za su samu a shekarar 2009 zai ninka sau daya idan an kwatanta su da na shekarar 2006. A waje daya kuma, a cikin shekaru 3 masu zuwa, kasar Sin za ta samar wa kasashen Afirka rancen kudin da yawansa zai kai dalar Amurka biliyan 3 a kan kudin ruwa kadan. Bugu da kari kuma, kasar Sin za ta ba da rancen kudin da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 2 tare da nuna gatanci ga masu saye-saye na kasashen Afirka. Sa'an nan kuma, za a kafa asusun neman bunkasuwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Daga karshe dai, jimlar kudaden wannan asusu za ta kai kudin dalar Amurka biliyan 5 a kai a kai.

Sauran manufofi 5 su ne, kasar Sin za ta ba da taimakon kyauta wajen gina cibiyar taron kungiyar tarayyar Afirka. Kuma za ta soke dukkan basusukan da take bin kasashen Afirka wadanda suke da dangantakar diplomasiyya da Jamhuriyar Jama'ar Sin, kuma suke cin basusuka masu tarin yawa har ma suke fama da talauci kwarai. A sa'i daya kuma, kasar Sin za ta kara bude kasuwanninta ga kasashen Afirka. Kasar Sin ba za ta buga harajin kwastam ba kan kayayyakin da ire-irensu za su kai 440, amma ba 190 kawai na yanzu ba da kasashen Afirka wadanda suke da dangantakar diplomasiyya da kasar Sin, kuma suke fama da talauci kwarai ke fitar da su zuwa kasar Sin. A cikin shekaru 3 masu zuwa, kasar Sin za ta kafa shiyoyyin yin hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya guda 3 ko 5 a kasashen Afirka. Bugu da kari kuma, kasar Sin za ta horar da kwararru dubu15 domin kasashen Afirka.

A gun bikin kaddamar taron, Mr. Meles Zenawi, firayin ministan kasar Habasha wadda ke shugabantar wannan taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka tare da kasar Sin, da kuma Denis Sassou-Nguesso, shugaban kasar Congo Kinshasha, kuma shugaba na yanzu na kungiyar tarayyar Afirka su ma sun bayar da jawabai bi da bi. (Sanusi Chen)