Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-04 08:32:08    
Kungiyoyin wakilan kasashen Afirka duk sun iso Beijing

cri
A ran 4 ga wata da sassafe, jirgin sama da shugaba Isaias Afwerki ya dauka ya iso birnin Beijing. Sakamakon haka, dukkan kungiyoyin wakilan kasashen Afirka 48 da wakilan kungiyar Tarayyar Afirka sun iso nan Beijing domin halartar taron koli da taron ministoci na 3 na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka da ake yi yanzu.

Ya zuwa yanzu, shugabanni 35 da firayin ministoci 6 tare da wani mataimakin shugaba na kasashen Afirka 42 sun riga sun iso nan Beijing domin halartar taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka da za a fara yi a ran 4 ga wata. Wakilan kungiyoyin kasa da kasa ciki har da na M.D.D. ma sun iso nan Beijing daya bayan daya.

Taken da aka tsara wa wannan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka shi ne, "sada zumunta da yin hadin guiwa da kuma samun cigaba tare tsakanin Sin da Afirka cikin lumana". Shugabannin kasar Sin da kasashen Afirka za su amince da raya sabuwar alakar dangantakar abokantaka bisa manya tsare-tsare tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da kuma tsara shirin neman hakikanin hadin guiwa a tsakaninsu a nan gaba. (Sanusi Chen)