Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-03 18:56:33    
'Yan jaridun kasashen waje sun yi yabo ga taron koli da za a yi a nan birnin Beijing

cri

Yanzu lokacin ya kusa da za a bude taron koli na dandalin hadin gwiwar tsakanin kasashen Sin da Afirka, 'yan jaridun waje sun yi yabo ga wannan taron koli bi da bi a kwanakin baya ta hanyoyin ba da labari, bayyani ko sharho.

Jaridar "al Ahram" da "kamfanin dilancin labaru na tsakiya ta gabas" na kasar Masar sun ce, taron koli na wannan karo wani taro mafi babba kuma mafi koli a tsakanin kasashen Sin da Afirka tun daga kasar Sin ta kafa mulkinta.

'Yan jarida na kasar Zimbabwe sun yaba wannan taron koli zai zama "abin tunawa ga abokantaka a tsakanin kasashen Sin da Afirka".

Jaridar "Union" ta kasar Gabon ta ce, nufin taron koli na Beijing shi ne kara hadin gwiwar da ke tsakanin kasashe masu tasowa da shawarwarin da ke tsakanin shugabannin kasashen Sin da Afirka. Kafuwar inuwa ta dandalin hadin gwiwar ta nuna karfin manufofin da kasar Sin take tafiya a kasashen Afirka.

Jaridar "Fraternit'e-Matin" ta kasar Cote d'Ivoire ta ambato maganar Mr. Fologo shugaban kwamitin zaman al'umma da tattalin arziki na kasar cewa, wannan taron koli yana da muhimmanci sosai ga kasashen Afirka wadanda ke karkashin halin cudanyar habakar kasashen duniya. Saboda kullum kasar Sin tana goyon bayan kasashen Afirka kan fannonin siyasa, tattalin arziki da harkokin waje.

Ban da haka kuma, jaridar "International Herald Tribune" ta kasar Amurka da jaridar "Nouvelles D'europe" ta kasar Faransa sun yi yabo ga taron koli na wannan karo sosai.