Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-03 16:28:49    
Dandalin hadin kan Sin da Afirka ya samar da wani kyakkyawan dandali ga kamfanonin Sin da ke Afirka

cri

Daga ran 3 zuwa ran 5 ga watan nan da muke ciki a nan birnin Beijing, za a yi taron koli na dandalin hadin kan Sin da Afirka, wato taron ministoci na karo na uku na dandalin. A daidai lokacin da aka cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da kasashen Afirka, mene ne bikin zai kawo wa kamfanonin kasar Sin da ke a Afirka? kuma yaya kamfanoni masu jarin kasar Sin suke bunkasa a Afirka? Domin amsa wadannan tambayoyi, wakilinmu ya yi hira da mataimakin manajan kamfanin gina tashar jiragen ruwa na kasar Sin, Mr.Lin Yichong.

Da ganin wakilinmu, sai Mr.Lin ya tabo magana a kan taron koli na dandalin hadin kan Sin da Afirka. Ya yi farin ciki ya gaya mana cewa, 'muna son yin amfani da wannan dandalin, don nuna karfin kamfaninmu, kuma dandalin ya samar da dama mai kyau gare mu wajen yin mu'amala da aminanmu na Afirka dangane da zumuncin da ke tsakanin bangarorin biyu da ayyukan gine-gine da dai sauran batutuwa, kuma dandalin zai amfana wa bangarorin biyu wajen samun damar hadin gwiwa da kara fahimtar juna a tsakaninsu.'

Mr.Lin ya ci gaba da cewa, yanzu an riga an shirya dandalin har sau biyu, kuma taron koli na Beijing zai zama karo na uku. Dandalin ya riga ya zama wani tsari na yin shawarwari tsakanin Sin da Afirka a kai a kai. Batutuwan da bangarorin biyu suka tattauna a gun taron dandalin da yarjejeniyoyin da suka kulla da kuma matakai da manufofin da aka gabatar dukansu suna da nasaba kwarai da kamfanoni. Sabo da haka, kamfanin gina tashar jiragen ruwa ta kasar Sin ya mai da hankali sosai a kan labaran da suke shafar dandalin, kuma yana yin amfani da sharuda masu kyau da dandalin ya samar wadanda za su amfana wa hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin bangarorin biyu. A yayin da ake yin wannan taron dandalin, a jibi, wato ran 3 ga wata, shugaban kasar Somaliya wanda ya zo kasar Sin don halartar taron dandalin, zai kai ziyara a kamfanin nan na gina tashar jiragen ruwa na kasar Sin, don tattauna yadda za a inganta hadin gwiwa a tsakanin kamfanin da kasar Somaliya.

A ganin Mr.Lin Yichong, mataimakin manajan kamfanin gina jiragen ruwa na kasar Sin, taron dandalin hadin kan Sin da Afirka da ake kokarin shiryawa wani misali ne na kwarai da zai bayyana kyakkyawar huldar da ke tsakanin Sin da Afirka a halin yanzu. A cikin 'yan shekarun nan baya, bi da bi ne kamfanin gina tashar jiragen ruwa na kasar Sin ya dauki nauyin wasu manyan ayyuka na Nijeriya, ciki har da yasar hanyar jiragen ruwa ta Calabar da gina tashar ruwa ta Sudan da dai sauransu, bisa bunkasuwarsa a cikin shekaru gomai da suka wuce, kamfanin ya sami sakamako mai kyau a wajen ayyukan teku daban daban, har ma ya zama wani babban kamfanin da ya shahara a kasashen Nijeriya da Sudan da Angola da dai sauran kasashen Afirka.

Manyan nasarorin da kamfanin gina tashar jiragen ruwa na kasar Sin ya samu ya zama wani misali na bunkasuwar kamfanoni masu jarin kasar Sin a Afirka, haka kuma sun bayyana nasarorin da aka samu a hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin Sin da Afirka. Yayin da yake amsa tambayarmu ta 'me ya sa Sin da Afirka suna iya samun nasara tare a hadin gwiwar da ke tsakaninsu, Mr.Lin ya ce, da farko dai, sharudansu sun tabbatar da ko wanensu yana iya nuna fifikonsu, su taimaki juna. Na biyu kuwa, kamfanoni masu jarin kasar Sin sun mai da hankali a kan al'adun kasashen Afirka, kuma suna kokarin kawo wa jama'ar wurin alheri cikin sahihanci. Ya ce,'Yawancin kasashen Afirka suna cikin kwanciyar hankali. Irin wannan kwanciyar hankali shi ya sa suke kishin bunkasa tattalin arzikinsu. Ko jam'iyyun da ke rike da ragamar mulki ko kuma jama'a, dukansu sun gane cewa, ba za a iya kara tabbatar da kwanciyar hankali ba, sai dai da bunkasuwar tattalin arziki, hakan nan kuma za a iya dinga kyautata zaman rayuwar jama'a.'

Wani dalilin da ya sa kasashen Sin da Afirka suka iya cimma nasara tare shi ne, sabo da kamfanoni masu jarin kasar Sin suna mai da hankali a kan sada zumunta a tsakaninsu da mazaunan Afirka, kuma suna girmama al'adunsu. Game da batun, Mr.Lin ya ce,'Duk inda muka tafi, mun mai da hankali a kan al'adun wurin, kuma muna girmama al'adun mazaunan wurin. A cikin shekarun nan da dama da muke gudanar da harkoki a Afirka, muna zauna lafiya da hukumomin wurin da kuma jama'arsu.'

Mr.Lin ya kuma ba mu wani misali. A lokacin watan Azumi, Mr.Lin ya kai ziyara a filayen ayyukansu da ke Sudan. Musulmi na Sudan sun karbe shi a matsayin wani babban bako, kuma sun ba shi abin shayi. Amma Mr.Lin ya sani cewar, musulmi ba su iya ci ko sha a rana a lokacin Azumi, shi ya sa Mr.Lin ya nuna godiya amma bai dauka ba. Abin nan ya burge mutanen Sudan kwarai, a ganinsu, Sinawa sun nuna musu girmamawa, kuma Sinawa sun mayar da su aminai, suna taimakonsu da sahihin zuci. Ban da kamfanin gina tashar jiragen ruwa na kasar Sin, sauran kamfanoni masu jarin kasar Sin su ma suna mai da hankali a kan huldar da ke tsakaninsu da mazaunan wurin, kuma suna zama jituwa da juna. Sabo da haka, bangarorin biyu ba ma kawai sun ci riba a fannin tattalin arziki ba, haka kuma sun inganta zumuncin da ke tsakaninsu. Sabo da haka, ma iya cewa, kamfanonin kasar Sin a Afirka sun zama muhimmin rukunin da ke inganta zumunci da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka.

Mr.Lin ya kuma ci gaba da cewa, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci sosai a kan huldar da ke tsakaninta da Afirka. a shekarar da muke ciki, shugaba Hu Jintao da firaminista Wen Jiabao na kasar Sin sun kai ziyara a Afirka daya bayan daya, kuma an kara ciyar da huldar siyasa a tsakanin bangarorin biyu gaba. A nasu bangaren kuma, kamfanonin kasar Sin da ke Afirka su ma suna kokarin bauta wa jama'ar wurin, don kara inganta zumunci da hadin gwiwar da ke tsakanin bangarorin biyu. Mr.Lin ya ce,'A watan Satumba na shekarar da ta gabata, a gun babban taron M.D.D., shugaban kasar Sin Hu Jintao, ya dauki alkawarin cewa, za a bai wa kasashen Afirka rancen kudin mai gatanci da yawansu ya kai dallar Amurka biliyan 10 a cikin shekaru uku masu zuwa, don tallafa wa manyan ayyuka na kasashen Afirka.' Sabo da haka, kamfanin gina tashar jiragen ruwa na kasar Sin ya kara karfin bauta wa Afirka. Ban da samar da taimakon kudi, kamfanin ya kuma ba da taimako ga kasashen Afirka a fannonin zane-zane da sayayya da samun kwangila da dai sauransu. Bayan haka, kamfanin ya kuma yi iyakacin kokarin samar da guraben aiki ga kasashen Afirka, yana daukar ma'aikatan wurin yadda ya kamata. Ban da ma'aikata, yana kuma kokarin sayen kayayyakin gine-gine a wurin.

Kamfanin gina tashar jiragen ruwa na kasar Sin wani misali ne na kamfanoni masu jarin kasar Sin da ke Afirka. Yana bauta wa Afirka cikin sahihanci, ya sami girmamawa daga kasashen Afirka, kuma kasashen Afirka suna son yin hadin gwiwa da shi. Sabo da haka, muna iya imani da cewa, ya kasance da kyakkyawar makoma a hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka. (Lubabatu)