Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-03 14:46:57    
Sabunta:An bude taron ministoci na karo na 3 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka

cri

Ran 3 ga wata, a nan Beijing, an bude taron ministoci na karo na 3 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wakilan kasar Sin da na dukan kasashe 48 na Afirka mambobin dandalin sun halarci wannan taro.

Mataimakiyar firayin ministar kasar Sin madam Wu Yi ta shugabanci taron ta kuma yi jawabin cewa, dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka muhimmin mataki ne da bangarorin Sin da Afirka suke dauka tare bisa muhimman tsare-tsare don daidaita kalubale da suke fuskanta a cikin sabon karni da karfafa huldar abokantaka ta gargajiya da kara yin hadin gwiwa don moriya juna. Ya kamata bangarorin 2 su rika kyautata tsarin dandalin tattaunawar da sa kaimi kan yin hadin gwiwa a tsakaninsu a cikin tsarin dandalin tattaunawar, bisa ka'idojin yin shawarwari cikin zaman daidai wa daida da moriyar juna daukan matakai sannu a hankali yadda ya kamata.

Ministan harkokin waje na kasar Habasha Seyoum Mesfin ya yi jawabi a madadin kasashen Afirka da cewa, huldar abokantaka ta muhimman tsare-tsare da ke tsakanin Sin da Afirka tana da muhimmiyar ma'ana ta manyan tsare-tsare. A matsayin kasar da ke gama kanta da kasar Sin wajen shugabantar dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, kasar Habasha za ta yi iyakacin kokarinta a fannin tabbatar da ganin cewa, taron kolin nan zai ci nasara.

A gun taron ministocin da aka yi a yau, an dudduba da kuma zartas da shirin doka na 'sanarwar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka' da na 'shirin ayyuka na Beijing na shekarar 2007 zuwa ta 2009' na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da kuma shirin dokar ajandar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, sa'an nan kuma, za a gabatar da wadannan shirye-shiryen dokoki ga taron koli na Beijing don duddubawa.(Tasallah)