Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-03 14:41:06    
Hu Jintao ya gana da shugabannin kasashen Afirka biyar bi da bi

cri

A ran 3 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da takwaransa na kasar Congo Brazzaville da na kasar Uganda da na kasar Saliyo da na kasar Ruwanda da kuma na kasar Ghana bi da bi wadanda suka zo birnin Beijing don halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka.

A cikin ganawar, shugaba Hu ya nuna godiya ga kasashen biyar da suke tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya. A waje daya kuma ya bayyana cewa, yin taron koli na Beijing cikin nasara yana da muhimmiyar ma'ana wajen kara fahimta da amincewa tsakanin shugabannin Sin da Afirka, da kara zumuncin gargajiya tsakanin Sin da Afrika, da inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka daga dukkan fannoni, da kuma kara hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa.

Shugabannin kasashen biyar sun bayyana cewa, kasar Sin aminiya ce da mutanen Afirka suka karbe ta sosai, sabo da haka gwamnatoci da jama'ar kasashen Afirka daban daban sun nuna yabo sosai ga taron.(Kande Gao)