Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-03 11:13:47    
Kasar Senegal tana fatan inganta hadin gwiwar tattalin arziki tare da kasar Sin

cri
A ran 2 ga wata, ministan kasuwanci na kasar Senegal Mamadou Diop wanda ya zo birnin Beijing na kasar Sin don halartar taron ministoci na uku na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ya yi bayani a gaban kafofin watsa labarai kafin ya tashi daga kasar, cewa kasar Senegal tana fatan za a iya ci gaba da ingiza hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da yankunan yammacin Afirka ta wannan taron ministoci.

Kuma Mr. Diop ya bayyana cewa, noman auduga wata sana'a ce da 'yan Afirka fiye da miliyan 100 suke yi domin zaman rayuwarsu. A yankunan yammacin Afirka kawai, ana iya samun auduga ton miliyan 2 a ko wace shekara, amma yawan auduga da ake iya sarrafawa a wurin ya kai kashi 5 cikin dari kawai. Kuma ya ce, kasar Sin tana nuna kwarewa sosai a fannin sarrafa auduga, shi ya sa ta iya hadin kai tare da kasashen da ke yammacin Afirka a fannin sarrafa auduga domin moriyar juna. Haka kuma wannan wani aiki ne da zai iya amfana da mutanen Afirka yayin da kamfanonin kasar Sin za su ci moriya.(Kande Gao)