Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-03 11:10:13    
Kafofin watsa labarai na kasashen Indiya da Kenya da Afirka ta Kudu sun nuna yabo ga taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka

cri
Kafin a kira taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, kafofin watsa labarai na Indiya da Kenya da Afirka ta Kudu sun buga labarai don nuna yabo ga taron.

A ran 2 ga wata, jaridar Hindu ta bayar da labari cewa, kasar Sin ta bude kofarta ga kasashen Afirka, kuma bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ta kawo wa nahiyar Afirka alheri. Kasar Sin ta ba da taimako sosai ga Afirka wajen gina hanyoyin motoci da na jiragen kasa da kuma asibitoci da dai sauransu, ban da wannan kuma ta samar da taimako ga Afirka wajen fasahohi. Sabo da haka ko shakka babu wannan taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wani mataki ne da ake dauka wajen ci gaba da inganta dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka.

Haka kuma a ranar, jaridar The Nation ta kasar Kenya ta nuna cewa, makasudin yin taron shi ne inganta zumunci da dangantakar hadin gwiwa da ta cinikayya tsakanin bangarorin biyu. Bunkasuwar dangantakar siyasa da tattalin arziki tsakanin Sin da Afirka cikin sauri ta jawo hankulan duk duniya.

Ban da wannan kuma a ran 1 ga wata, jaridar Business Day ta kasar Afirka ta Kudu ta bayyana cewa, ko da yake ba a kafa dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka cikin dogon lokaci ba, amma yana samun bunkasuwa sosai, yanzu ya riga ya zama wani muhimmin wuri ne da Sin da Afirka suke tattaunawa tare, da kuma wani tsari mai amfani wajen hadin gwiwa tsakanisu.(Kande Gao)