Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-03 11:07:13    
Shugabannin kasashen Afirka 15 sun iso birnin Beijing a ran 2 ga wata

cri
A ran 2 ga wata da safe, daya bayan daya shugaban kasar Zambia Levy Patrick Nwanawasa, da shugaban kasar Camerron Paul Biya, da shugaban kasar Saliyo Alhaji Ahmad Tejan Kabbah, da shugaban kasar Ghana John Agyekum Kafuor, da shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki, da shugaban kasar Nijer Mamadou Tandja, da firayim ministan kasar Morocco Driss Jettou, da kuma shugaban kasar Mali Amadou Toumani Toure sun iso birnin Beijing, babban birnin kasar Sin.

Haka kuma a ranar da yamma da dare, shugaban kasar Somaliya Abdullahi Yusuf Ahmed, da shugaban kasasr Uganda Yoweri Museveni, da shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame, da shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe da mataimakin shugaban kasar Congo Kinshasa Yerodia Ndombasi sun iso birnin Beijing bi da bi.

A ranar kuwa, firayin ministan kasar Angola Fernando Dos Santos, da shugaban kasar Congo Brazzaville Denis Sassou-Nguesso su ma sun iso birnin Beijing bayan da suka kammala yin ziyarar a birnin Shanghai na kasar Sin domin halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi a ran 4 ga wata. Ya zuwa yanzu shugabannin kasashen Afirka 24 sun riga sun iso kasar Sin don halartar taron.(Kande Gao)