Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-03 09:14:10    
Shugaba Hu Jintao ya gana da takwarorinsa na Botswana da Sudan

cri
Ran 2 ga wata, a nan Beijing, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da takwarorinsa na kasashen Botswana Festus Mogae da na Sudan Omar Hassan El-Bashir, wadanda za su halarci taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

A gun ganawar da aka yi, Mr. Hu ya bayyana cewa, don daga matsayin hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka, bangarorin 2 sun tsai da kudurin yin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, makasudinsu shi ne domin manyan jami'ai su tattauna da tsara shiri kan manyan manufofi kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, kuma su tabbatar da manufa wajen yin hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2 daga fannoni daban daban a nan gaba. Mr. Mogae da Mr. El-Bashir sun bayyana cewa, jama'ar kasashen Afirka suna samun alheri daga wajen yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. Manufar da kasar Sin ta tsayar don kara yin hadin gwiwa da kasashen Afirka tana da muhimmanci sosai ga bunkasuwar Afirka. Shugabannin kasashen 3 sun yi bayanin cewa, za su yi kokari tare wajen sa kaimi kan taron koli na Beijing da ya samu nasara, kuma ingiza hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka a fannoni daban daban zuwa sabon mataki.(Tasallah)