Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-02 21:30:35    
Kasar Sin ta tura kungiya mai girma ta matasa masu aikin sa kai zuwa Afirka

cri

A jiya ranar 1 ga wata, matasan kasar Sin 50 sun isa Afirka, kuma sun fara yin hidimomi a kasar Habasha a matsayinsu na masu aikin sa kai. Wadannan matasa masu aikin sa kai rukuni na biyu ne da kasar Sin ta tura zuwa kasar Habasha, haka kuma kungiyar nan kungiyar masu aikin sa kai ce mafi girma da kasar Sin ta taba tura zuwa kasashen waje har zuwa yanzu. Nan da shekara guda, za su gudanar da ayyukan hidima ga jama'ar kasar Habasha a fannonin koyar da Sinanci da gina kauyuka da kiwon lafiya da dai sauransu kuma ba tare da biyan kudi ba.

Tun daga shekarar da ta gabata, kasar Sin ta fara aikawa da matasa masu aikin sa kai zuwa Afirka. Yawan matasa masu aikin sa kai da kasar Sin ta tura zuwa Afirka a cikin rukuni na farko ya kai 12 gaba daya, kuma kasar da suka je ita ce Habasha. A can wurin, sun yi wa majiyyata Acupuncture, sun yada fasahar samun iskar gas daga taki, sun kuma koyar da harshen Sinanci a jami'o'i. A wa'adin aikinsu na rabin shekara, wadannan masu aikin sa kai 12 sun sami yabo sosai daga gwamnatin Habasha da kuma jama'arta.

Ga shi yanzu, an kara samun matasan kasar Sin 50 da suka tafi Habasha, inda za su shafe shekara guda suna ba da hidimomi cikin sa kai. Zhong Qiuping, yarinyar da ta samu digiri na biyu ba da dadewa ba a jami'ar koyon fasahar noma ta kasar Sin, tana daya daga cikinsu. Ta ce, tana fatan za ta iya yin amfani da abin da take kwarewa a kai don bauta wa Habasha.'ina fatan zan iya zuwa kauyukan kasar Habasha, bisa abin da na koya, ko daga tsare-tsaren kauyuka ko kuma daga fannin bakatun manoma da kuma raya karfinsu, in yi musu hidima a hakika.'

Daidai kamar yadda malama Zhong Qiuping take, sauran matasa masu aikin sa kai su ma sun je Afirka ne don neman cimma burinsu na bauta wa Afirka.

Kaleb Tesfaye, wani saurayin kasar Habasha ya ce, jama'ar Habasha suna farin ciki da ganin zuwan Sinawa masu aikin sa kai. Ya ce,'Habasha kasa ce mai tasowa, kuma ita kasar Sin tana da dimbin fasahohi masu kyau da ya kamata Habasha ta yi koyi da su. A ganina, tura masu aikin sa kai zuwa kasarmu da kasar Sin ta yi, zai amfana wa bunkasuwar kasarmu kwarai.'

Wani abin da ya kamata mu mai da hankali a kai shi ne, wadannan masu aikin sa kai na kasar Sin 50 sun je Habasha ne a daidai lokacin da za a shirya taron dandalin hadin kan Sin da Afirka, wato lokacin da bangarori daban daban ke kokarin tattauna hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka. Mr.Wei Jianguo, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya ce, sabo da haka ne, zuwan wadannan masu aikin sa kai na kasar Sin a Afirka yana da muhimmiyar ma'ana.'A lokacin da za a kira taron dandalin hadin kan Sin da Afirka, gwamnatin kasar Sin ta tura wadannan matasa masu aikin sa kai zuwa kasar Habasha, wannan ya bayyana zumuncin jama'ar kasar Sin ga jama'ar Habasha da ma jama'ar Afirka baki daya, haka kuma ya bayyana babban burin gwamnatin kasar Sin da na jama'arta na kara inganta hadin gwiwar aminci a tsakaninsu da jama'a da gwamnatoci na kasashen Afirka daban daban.'

Mr.Wei ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Sin ta aika da matasa masu aikin sa kai zuwa kasashe masu tasowa ne don gudanar da ayyukan hidima ga hukumomi da kuma jama'ar wurin a fannonin kiwon lafiya da ilmantarwa da dai sauransu, su manzanni ne masu sada zumunta na jama'ar kasar Sin. A nan gaba, bisa bukatun kasashen da abin ya shafa, gwamnatin kasar Sin za ta kara kasashen da za ta tura masu aikin sa kai.(Lubabatu)