Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-02 21:11:57    
Kasar Sin za ta ci gaba da taimakon kasashen Afrika wajen shawo kan cutar zazzabin sauro

cri
Ran 2 ga wata, Malam Chong Quan, kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da taimakon kasashen Afrika wajen kara kwarewarsu don shawo kan cutar zazzabin sauro ta hanyoyi daban daban.

A gun taron watsa labaru da aka shirya a birnin Beijing, Malam Chong Quan ya ce, nan gaba, kasar Sin za ta kara inganta hadin kai a tsakaninta da kasashen Afrika a fannin shawo kan cutar zazzabin sauro, ta yi shirin kafa cibiyoyi a kasashen Afrika da ke fama da cutar nan mai tsanani don gwada kyakkyawan misali ga shawo kan cutar. Sa'an nan za ta samar da magungunan cutar zazzabin sauro ga kasshen Afrika da ke yaki da cutar ba tare da biya ko kwabo daya ba. Ka zalika kasar Sin za ta kara haorar da jami'an kula da harkokin kiwon lafiya da wadanda ke kula da asibiti da magungunan sha domin kasashen Afrika.

Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta samar da magungunan cutar zazzabin sauro ga kasashen Afrika sama da goma kamar Nijeriya da Somali da Nijer da Togo da kasar Afrika ta tsakiya da Kamaru da sauransu ba tare da biya kobo ko daya ba. (Halilu)