Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-02 20:53:17    
Taron Koli zai ba da gudummawa a zahiri wajen hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka a cewar shugabannin kasashen Afirka

cri

Ran 2 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Hadj Omar Bongo shugaban kasar Gabon ya gaskata cewa, wannan taron Koli zai ba da gudummawa a zahiri wajen hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka?Mr. Bongo ya nuna haka yayin da yake ganawa da manema labaru na gidan rediyonmu.

Mr. Bongo ya ce, wannan taron koli zai sa kaimi ga bunkasuwar hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka, kuma cigaba da bunkasuwar huldar da ke tsakaninsu. Ya ce, kasar Gabon tana son ta kara hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin kan fannonin manyan gine gine, hanyoyin sadarwa da tattalin arziki, kuma ta yi maraba da 'yan kasuwa na kasar Sin su zuba jari a kasar Gabon, kuma yana fatan zai kara yin tattaunwa tare da bangaren kasar Sin kan makomar hadin gwiwarsu kan tattanin zrziki da ciniki, ta yadda don neman bunkasuwar kasashen biyu tare.

Ran 2 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. James Michel shugaban kasar Seychelles ya gana da daliban kasar da suke yin karatu a kasar Sin inda ya ce, jama'ar kasar Sin abokan jama'ar kasar Seychelles ne.

Mr. Michel ya ce, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta kut da kut kan fannoin ciniki da al'adu, yawan daliban da suke son su yi karatu a kasar Sin ya yi ta karuwa.