Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-02 20:49:38    
Kasar Sin za ta kara kokari wajen inganta hadin kai a tsakaninta da kasashen Afrika

cri

A kwanakin baya, wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya kai ziyara ga Malam Liu Guijin, jakadan kasar Sin da ke wakilci a kasar Afrika ta Kudu don jin ta bakinsa, sai ya bayyana cewa, nan gaba kasar Sin za ta kara kokari wajen ba da taimako ga kasashen Afrika.

Ya ce, yayin da Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ke yin ziyara a kasar Afrika ta Kudu a watan Yuni da ya wuce, kasashen biyu sun cimma yarjejeniya game da batun kayyade yawan kayayyakin saka da kasar Sin ke fitarwa zuwa kasar Afrika ta Kudu. Ko da yake a karkashin yarjejeniyar, yawan kayayyakin saka da masana'antun kasar Sin ke fitarwa zuwa kasar Afrika ta Kudu zai ragu, amma irin wannan mataki da gwamnatin kasar Sin ta dauka, yana kan matsayin irin matakin sahihanci da kasarmu ke nuna wa Afrika.

Gwamnatin kasar Sin ta yi la'akari sosai da matsi da gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ke sha a kan batun kayayyakin saka, ta cim ma yarjejeniyar, sabo da haka ta sami yabo daga wajen bangarori daban daban, duk da gunaguni da wasu 'yan tireda na kasar suka yi. Malam Liu Guijin ya ci gaba da cewa, "za mu kara daukar hakikanan matakai don bayyana cewa, kasar Sin aminiya da babbar abokiya ce ga Afrika."

A ganinsa, Kasar Sin da kasashen Afrika dukanninsu kasashe masu tasowa ne, ayyukan da suke fuskanta iri daya ne, kuma matsayinsu da ra'ayoyinsu ma iri daya ne ko kusan daya a kan manyan batutuwan duniya, suna iya taimakon juna sosai a fannin tattalin arziki, duk wadannan sun mayar da kasar Sin da kasashen Afirka da su zama manyan abokai bisa manyan tsare-tsare.

Malam Liu Guijin ya bayyana cewa, hajojin kasar Sin da fasaharta sun fi dacewa da kasashen Afrika. Sabo da haka suna samun karbuwa sosai daga wajen jama'ar kasar Afrika ta Kudu. Dalilin da ya sa haka shi ne domin yawan kudi da ake kashewa wajen samunsu bai yi yawa ba, kuma ta hanyar nan za a kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar da sharudansu na sarrafa kayayyaki.

Dangane da surutun banza da ake barbazawa cewa, wai "kasar Sin na wasoson Afrika", Malam Liu Guijin ya ari bakin Malam Mucavele, babban direktan zartaswa na sakatariyar kula da sabon shirin abokantaka na raya Afrika, yana cewa, idan an dudduba sharuda da Turawa suka gabatar wajen hako ma'adinan Afrika a wancan zamani, sa'an an dudduba sharudan kasar Sin na kulla yarjejeniyoyin a tsakanin Sin da kasashen Afrika ciki har da Angola da Nijeriya, to, ko za a gano wata kasa daban wadda ta fi kasar Sin wajen ba da taimako ga kasashen Afrika? A'a. Bayan haka ya jaddada cewa, ko da yaushe, kuma ko ta yaya, ba za a iya dora wa kasar Sin "sabon mulkin mallaka" ba.

Malam Liu Guijin ya ci gaba da cewa, a gun taron koli na Beijing na dandalin tattauna kan hadin guiwar Sin da Afrika da za a yi a nan gaba kadan, gwamnatin kasar Sin za ta gabatar da wasu matakai da za ta dauka don kara ba da taimako wajen raya kasashen Afrika. Ya fayyace cewa, Shugaban kasar Afrika ta Kudu Mr Thabo Mbeki zai halarci taron koli na dandalin tattauna kan hadin guiwar Sin da Afrika da za a kira a farkon wannan wata a birnin Beijing. (Halilu)