Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-02 20:33:00    
Hadin kan Sin da Afrika yana amfana wa bangarorin nan biyu duka

cri
Ran 2 ga wata, a nan birnin Beijing, Malam Liu Chaochao, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, hadin kai da ake yi tsakanin Sin da Afrika don moriyar juna a fili kuma cikin daidaici yana amfana wa bangarorin nan biyu da jama'ar kasashen Afrika da abin ya shafa.

A gun taron manema labaru da aka saba yi, Malam Liu Jianchao ya kara da cewa, hadin kai da ake yi a tsakanin Sin da Afrika a fannoni daban daban yana samun goyon baya da amincewa daga wajen jama'ar Sin da jama'ar kasashen Afrika. Bangaren Sin ya jiku sosai da cewa, ko gwamnatocin kasashen Afrika ko kuma jama'arsu suna dokin kara inganta hadin kai a tsakanin Sin da Afrika. Yana kuma ganin cewa, manufar Sin dangane da ba da gudummuwa ga Afrika tana da gaskiya.

Haka nan kuma Malam Liu Jianchao ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana maraba da kasashen Afrika biyar wadanda ba su kulla huldar diplomasiya a tsakaninsu da kasar Sin ba, su ma za su aika da 'yan kallo wajen halartar taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika da za a yi nan gaba kadan a kasar Sin. (Halilu)