Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-02 17:29:44    
Shugabannin kasashen Afrika 8 sun iso nan birnin Beijing daya bayan daya

cri
Ran 2 ga wata da safe, Mr. Levy Patrick Mwanawasa, shugaban kasar Zambia, da Mr. Paul Biya, shugaban kasar Cameroom, da Mr. Ahmed Tejan Kabbah, shugaban kasar Saliyo, da Mr. John Kufuor, shugaban kasar Gana, da Mwai Kibaki, shugaban kasar Kenya, da Mamadou Tandja, shugaban kasar Niger, da Mr. Driss Jettou, firayin ministan kasar Morocco, da kuma Mr. Amadou Toumani Toure, shugaban kasar Mali, sun isa nan birnin Beijing na kasar Sin daya bayan daya, domin halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan harkokin hadin kai a tsakanin Sin da Afrika da za a bude a ran 4 ga wata.

Kafin wannan rana, shugabannin kasashe 11 na Afrika da suka fito daga kasashen Liberia, da Guinea-Bissau, da Angola, da Gabon, da Burundi, da Comoros, da Sudan, da Equatorial Guinea, da Botswana, da Kongo Brazzaville, da kuma Seychelles, sun riga sun isa kasar Sin daya bayan daya, ya zuwa yanzu, yawan shugabannin kasashen Afrika da suka isa kasar Sin don halartar taron koli ya kai 19. (Bilkisu)