Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-02 17:23:59    
An yi bikin kaddamar da kan sarki don tunawa da taron koli na Beijing

cri

Ran 2 ga wata, an yi bikin kaddamar da kan sarki don tunawa da taron koli na Beijing da taron ministoci na karo na uku na dandalin tattaunawa kan hadin guiwa a tsakanin Sin da Afrika, kuma an yi bikin bude nunin kayayyakin fasaha na Afrika, da nunin takardun kudade da tsabar kudi da kan sarki na kasashen Afrika.

An mayar da hoton tambarin taron koli na Beijing na dandalin tattauna kan hadin guiwa a tsakanin Sin da Afrika da ya zama babban hoto a kan jikin kan sarkin nan da aka kaddama a wannan rana. A takaice, kan sarkin ya gwada babban jigon taron kolin kamar haka "aminci da zaman lafiya da hadin kai da kuma bunkasuwa."

Haka zalika a gun nunin kayayyakin fasaha da Afrika danunin takardun kudi da tsabar kudi na kasashen Afrika, an nuna kayayyakin fasaha sama da 300 na kasashen Afrika da dama kamar sassakakkun kayayyakin katako da na tagulla da dutse da zane-zane da tangaran da sauransu, da takardun kudi da tsabar kudi da kan sarki da yawa na kasashen Afrika 48 wadanda suka kulla huldar diplolmasiya a tsakaninsu da Sin, ta yadda 'yan kallo za su gane al'adun Afrika da tabi'unta wadanda ba a iya samunsu a sauran wurare na duniya ba. (Halilu)