Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 2 ga watan nan , An rufe taron manyan jami'ai na 5 kan Dandalin hadin gwiwar tsakanin kasar Sin da Afrika a nan birnin Beijing
Wei Jianguo , sakataren Kwamitin shirya taron kolin Dandalin hadin gwiwar tsakanin Sin da Afrika kuma mataimakin Ministan harkokin Ciniki na Kasar Sin da Nolana Ta-Ama , shugaban Kungiyar jakadun kasashen Afrika da ke kasar Sin kuma jakadan kasar Togo dake kasar sun yi jawabi a gun bikin rufe taron .
Mr. Wei ya bayyana cewa , a cikin shekaru 6 da suka shige , Bayan da aka kafa dandalin hadin gwiwar tsakanin Sin da Afrika , hadin gwiwar tsakaninsu a fannoni daban daban ya sami yalwatuwa da saurin gaske . A gun taron kolin Beijing , shugabannin kasar Sin da na Afrika za su musaya ra'ayoyinsu sosai kan yadda za a kara bunkasa huldar dake tsakaninsu. Taron tabbas ne zai kara sabon karfi kan zumunci da hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afrika .
Mr. Ta Ama ya ce , wannan shekara cikon shekaru 50 ne da kasar Sin da kasashen Afrika suka kulla huldar diflomasiya . Taron kolin Beijing kan Dandalin hadin gwiwar tsakanin Sin da Afrika zai zama muhimmin batu a tarihin dangantakar tsakanin Sin da Afrika , kuma tabbas ne zai kara karfafa huldar dake tsakaninsu da ba da taimako ga karfafa zumunci da inganta hadin gwiwa da samun bunkasuwa tare . (Ado)
|