A ran 1 ga wata da dare, shugaban kasar Seychelles James Alix Michel ya iso birnin Beijing domin fara ziyarar aiki da kuma halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi a ran 4 ga wata.
A ranar kuma, shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir, da shugaban kasar Equatorial Guinea Obiang Nguema Mbasogo, da kuma Festus Mogae, shugaban kasar Botswana sun iso birnin Beijing, yayin da Denis Sassou-Nguesso, shugaban kasar Congo Brazzaville ya isa birnin Shanghai na kasar Sin.
Ya zuwa yanzu, shugabannin kasashen Afirka 11, wato Liberiya da Guinea Bissau da Angola da Gabon da Burundi da Comoros da Sudan da Equatorial Guinea da Botswana da Congo Brazzaville da Seychelles sun riga sun iso kasar Sin daya bayan daya don halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi a ran 4 ga wata.
Haka kuma shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka Alpha Oumar Konare ya iso birnin Beijing a ranar.(Kande Gao)
|