A ran 1 ga wata, yayin da shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ke yin ziyara a birnin Shenzhen na kasar Sin, ya bayyana cewa, kasar Budundi za ta aiwatar da manufar bude kofarta ga kasashen waje, kuma tana fatan kamfanonin kasar Sin masu yawa za su je kasar don zuba jari.
Lokacin da yake ganawa da Liu Yingli, mataimakin magajin birnin Shenzhen, shugaba Nkurunziza ya bayyana cewa, kasar Burundi ta fitar da kanta daga yake-yake na shekaru 10 ba da jimawa ba, yanzu tana farfado harkokin raya tattalin arziki da sha'anin kasuwanci, da kuma aiwatar da manufar bude kofarta ga kasashen waje. Kasar Burundi tana fatan za ta iya koyon fasahohi masu zamani na kasar Sin, haka kuma tana fatan kamfanonin kasar Sin masu yawa za su je kasar domin zuba jari da samun bunkasuwa.(Kande Gao)
|