Wakilin rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , A ran 1 ga watan nan a Gidan ajiye kayayyakin tarihi na birnin Pretoria , hedkwatar hukumomin Kasar Afrika ta Kudu , An bude Bikin manyan musaye-musayen al'adu kan kasar Sin .
A gun taron bude bikin , Cai Wu , Darektan Ofishin labaru na Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa , musaye-musayen al'adu muhimmin kashi ne na hadin gwiwar tsakanin Kasar Sin da kasar Afrika ta kudu , kuma hanya ce ta karfafa fahimtar juna tsakanin jama'ar kasashen biyu . Gwamnatin kasar Sin tana fatan za a tabbatar da tunanin bunkasuwar cikin lumana da samun wadatuwa tare da kafa duniya mai jituwa ta hanyar yin musaye-musaye masu yawa da kasashen Afrika .
A gun taron , Pallo Jordan , ministan al'adu na kasar Afrika ta kudu ya ce , ta wannan bikin kan kasar Sin , jama'ar kasar Afrika ta kudu za su kara fahimtar al'adu da fasahohi da falsafa da sauransu na kasar Sin . (Ado)
|