Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-01 21:34:02    
Shugaban kasar Sin ya yi shawarwari da shugabannin kasashen Afirka

cri
A yau ran 1 ga wata a nan birnin Beijing, bi da bi ne shugaban kasar Sin, Hu Jintao ya yi shawarwari tare da takwarorinsa na kasashen Guinea-Bissau da Liberia, wato Mr.Bernardo Vieira da Madam Ellen Johnson-Sirleaf, wadanda suka zo nan kasar Sin don yin ziyarar aiki da kuma halartar taron kolin dandalin hadin kan Sin da Afirka. Bayan haka, Mr.Hu Jintao ya kuma gana da shugaba El Hadj Omar Bongo na kasar Gabon da shugaba Ahmed Abdallah Mohamed Sambi na kasar Comoros da kuma shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka, Alpha Oumar Konare, daya bayan daya.

Yayin da yake yin shawarwari tare da Mr.Vieira, shugaban kasar Guinea Bissau, Mr.Hu ya jaddada cewa, ya kamata kasashen biyu su tsaya kan moriyar juna da kuma ci gaba tare, su inganta hadin gwiwa a tsakaninsu bisa tsarin dandalin hadin kan Sin da Afirka. A yayin da yake yin shawarwari da Madam Johnson-Sirleaf kuma, Mr.Hu ya ce, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka a kan goyon bayan aikin shimfida zaman lafiya a Liberia da kuma farfado da tattalin arzikin kasar, kamata ya yi kasashen biyu su zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a tsakaninsu, kuma su habaka cinikinsu.

Bayan haka, a yayin da yake ganawa da Mr.Bonga da Mr.Sambi da kuma Mr.Konare, Mr.Hu Jintao ya bayyana cewa, taron koli na dandalin hadin kan Sin da Afirka wani kasaitaccen biki ne a tarihin huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka, ko shakka babu zai zama wani muhimmin al'amari a tarihin bunkasuwar Sin da Afirka, kuma zai kara share fage ga bunkasuwar huldar Sin da Afirka.

A nasu bangaren kuma, shugabannin Afirka sun ce, har kullum kasar Sin yana girmama kasashen Afirka da kuma taimakonsu, kuma ba ta tsoma baki cikin harkokin gida na kasashen Afirka, ita sahihiyar abokiya ce da kasashen Afirka ke iya dogara. Sun ci gaba da cewa, za su hada gwiwarsu da Sin wajen neman cimma nasarar taron kolin dandalin hadin kan Sin da Afirka da kara dankon zumunci a tsakanin Afirka da Sin da kara bunkasa mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninsu.

A ranar kuma, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao shi ma ya gana da shugabannin kasashen Guinea-Bissau da Liberia bi da bi.(Lubabatu)