Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-01 20:48:48    
Takaitaccen bayani kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka

cri

Tun daga ran 3 zuwa ran 5 ga watan Nuwamba, za a kira taron koli da taron ministoci na taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Yanzu, ga wani takaitaccen bayani kan dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Dangantakar sada zumunta a tsakanin Sin da kasashen Afirka tana nan dadewa tare da kuma tushe mai karfi domin suna da kwatakwacin tarihi. Lokacin da suke neman 'yancin kan al'ummarsu, kasar Sin da kasashen Afirka sun nuna wa juna goyon baya da tausayi.

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin da yantattun kasashen Afirka, dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ta kai wani sabon mataki. A cikin shekaru 50 da suka wuce, dangantakar siyasa a tsakaninsu tana ta samun karfafuwa. Muhimman jami'ai nasu suna kai wa juna ziyara a kai a kai. Dangantakar hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya ma tana samu cigaba cikin sauri. Bugu da kari kuma, sun mai da hankali sosai kan yadda za su kara yin shawarwari da musayar ra'ayoyinsu kan harkokin kasa da kasa. Kasar Sin ta taba samar wa kasashen Afirka taimako iri iri bisa karfinta, kasashen Afirka ma suna nuna wa kasar Sin goyon baya a fanonni iri daban-daban.

Sada zumunta da zama tare cikin lumana da neman gama kai da hadin guiwa da kuma neman bunkasuwa tare, ka'idoji ne da ake bi lokacin da ake yin mu'ammala da hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka. Suna kuma kara sa kaimi wajen ciyar da dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka gaba ba tare da kasala ba.

Yaya shugabannin kasar Sin suke sharhi kan dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka.

A watan Afrilu na shekarar da muke ciki, lokacin da yake bayar da jawabi a gun majalisar dokokin kasar Nijeriya, Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya bayar da ra'ayoyi guda 5 kan yadda za a raya sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Wadannan ra'ayoyi 5 su ne, ya kamata a kara amincewa da juna kan harkokin siyasa da kara moriyar juna da neman bunkasuwa tare kan tattalin arziki, da a mai da hankali wajen fahimtar al'adu juna da kara yin hadin guiwa a fanning tsaron kai da kuma kara yin mu'ammala kan harkokin kasa da kasa.

Sa'an nan kuma, lokacin da yake gabatar da jawabi a gun taron dandalin tattaunawa kan yadda za a yi hadin guiwar kasuwanci a tsakanin kasar Sin da kasar Afirka ta kudu da aka yi a watan Yuni na shekarar da muke ciki lokacin da yake yin ziyara a kasar Afirka ta kudu, Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya ce, dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka tana daya daga cikin muhimman tushe ne ga ayyukan diplomasiyya da kasar Sin ke yi. Karfafa da raya dangantakar hadin guiwa irin ta sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka babban zabe ne da kasar Sin take yi bisa manyan tsare-tsare a cikin dogon lokaci. Kasar Sin za ta ci gaba da bin ka'idojin sada zumunta da zama tare cikin lumana da neman gama kai da hadin guiwa da kuma neman bunkasuwa tare, kuma za ta kara mai da hankali kan yadda kasar Sin da kasashen Afirka za su kara amincewa da juna kan harkokin siyasa da kara moriyar juna da neman bunkasuwa tare kan tattalin arziki, da a mai da hankali wajen sanin wa juna al'adunsu da kara yin hadin guiwa a fanning tsaron kai da kuma kara yin mu'ammala kan harkokin kasa da kasa domin cimma burin kafawa da raya sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninta da kasashen Afirka.

Bugu da kari kuma, a gun wani taron manema labaru da aka yi a birnin Alkahri lokacin da Wen Jiabao yake yin ziyara a kasar Masar, Mr. Wen ya taba bayyana manufofin Afirka da kasar Sin take dauka filla filla. Har ya rubuta wata rubutacciyar waka mai suna "Na koma garina" lokacin da yake kawo wa kasashen Afirka ziyara a watan Yuni na shekarar da muke ciki.

"Kasar Sin da kasashen Afirka aminai ne a kowane lokaci."

Kasar Sin kasa mai tasowa ce mafi girma a duk duniya. Tana neman samun bunkasuwa cikin lumana, kuma tana aiwatar da manufofin diplomasiyya mai zaman kanta cikin lumana. Sa'an nan kuma kasar Sin tana son kulla dangantakar sada zumunta da dukkan kasashen waje bisa ka'idojin zaman tare cikin lumana domin kara zumunci da hadin guiwa da kuma tabbatar da zaman lafiya mai dorewa da bunkasuwa a duk duniya.

Manufofin hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Lokacin da kasar Sin take raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninta da kasashen Afirka, ta fi mai da hankali wajen bin ka'idoji guda 3, wato, da farko dai, ta yi kokari kan yadda za a kara shigar da kayayyakin kasashen Afirka a kasuwar kasar Sin. Tun da haka, yanzu kasar Sin tana daukar matakan da za su iya sa kaimi ga kasashen Afirka da su sayar da kayayyakinsu a kasuwar kasar Sin. Sa'an nan, tana hada aikin samar wa kasashen Afirka taimakon kyauta da yin hadin guiwar fasaha a tsakaninta da kasashen Afirka, kuma ta fi mai da hankali kan yadda kasashen Afirka za su iya kyautata karfinsu wajen neman bunkasuwa da kansu. Bugu da kari kuma, kasar Sin tana taimaka wa kasashen Afirka wajen horar da injiniyoyi da kwararru iri iri.

"Babu barazana sai hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka".

Lokacin da Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin yake yin ziyara a kasashen Afirka 7, ya bayyana cewa, "Jama'ar kasar Sin aminiya ce ga jama'ar kasashen Afirka har abada. Kasar Sin ta raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ba domin kwace albarkatun halittu na kasashen Afirka kamar yadda wasu mutane suke fada ba." Wannan ra'ayin da Mr. Wen ya bayar ya samu amincewa daga kasashen Afirka duka.

Bana shekara ce ta cikon shekaru 50 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. A cikin wadannan shekaru 50 da suka wuce, kasar Sin ta yi kokari sosai wajen taimakawar kasashen Afirka da su ciyar da karfinsu gaba da kuma su nemi bunkasuwa da kansu. Sa'an nan kuma a cikin wadannan shekaru 50 da suka wuce, kasashen Afirka sun nuna wa kasar Sin goyon baya sosai kan muhimman batutuwa masu tarin yawa a gun taruruwa da kungiyoyi na duniya.

"Kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan matsayin samar wa kasashen Afirka taimako bisa karfinta amma ba tare da kowane sharadin siyasa ba." Yanzu abubuwa masu tarin yawa suna tabbatar da wannan maganar da Wen Jiabao ya yi a gun bikin kaddamar da taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasuwanci a tsakanin kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu. Ya zuwa yanzu, ayyukan raya tattalin arziki da zaman al'ummomin kasashen Afirka da kasar Sin ta samar musu taimakon kyauta sun kai kusan dari 9. A cikin shekaru 6 da suka wuce bayan kafuwar taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afirkam kasar Sin ta riga ta soke basusukan da take bin kasashen Afirka da yawansu ya kai kudin Sin yuan biliyan 10.5. Sa'an nan kuma, kasar Sin ta horar da kwararru iri iri fiye da dubu 10 don kasashen Afirka. A cikin wadannan shekaru 50 da suka wuce, yawan marasa lafiya na kasashen Afirka da suka samu jiyya daga likitocin kasar Sin dubu 16 ya riga ya kai kimanin miliyan 260.

Amma, a kan samar wa juna taimakawa. Kasar Sin ta kan fadi cewa, "kasar Sin tana bukatar Afirka". Marigayi shugaban kasar Sin Mao Zedong ya taba fadi cewa, aminan Afirka ne sun daga mu sai mu shiga M.D.D. A cikin membobi kasashe na M.D.D., da akwai kasashen Afirka 53, wato sun kai kashi 28 cikin kashi dari daga dukkan kujerun M.D.D. A kan batutuwan Taiwan da hakkin dan Adam, kuma da yunkurin neman izinin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympic da taron baje kolin duniya da kasar Sin ta yi, kowa ya gani, kasashen Afirka ne suna tsayawa tsayin daka kan matsayin nuna wa kasar Sin goyon baya.

Lokacin da Wen Jiabao yake waiwayar tarihin yin hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka da shugabannin kasashen Afirka, Mr. Wen ya ce, "Na zo gidan dangina ne, kuma na zo nan ne domin gai da aminanmu." Shugabannin kasashen Afirka sun kuma gaya masa cewa, "Ka dawo gidanka".

Cigaban da kasar Sin ta samu ta hanyar zaman lafiya, wannan ya kawo wa jama'ar kasashen Afirka imani da hanyar neman bunkasuwa. Mr. Femi Akomolefu, wani sanannen shehun malami ne na kasar Nijeriya ya rubuta wani bayani, inda ya ce, "Sauye-sauyen tattalin arzikin kasar Sin yana nan a gaban idanunmu", wannan "abin al'ajabi" ya bayyana cewa, "Wata al'ummar da ke cike da imani da niyya da kuma hangen nesa za ta iya samun cigaban da ya wuce abin da ake zata." Shugaba Dos Santos, shugaban kasar Angola ya kuma ce, "Matsayin da kasar Sin take dauka yana dacewa da halin da ake ciki. Wannan matsayi ma yana dacewa da kasashen Afirka. Kasar Sin ta samar wa kasashen Afirka taimako, ta kuma kafa dangantaka a tsakaninta da kasashen Afirka domin yunkurin ciyar da hadin guiwa irin ta taimaka wa juna a tsakaninta da kasashen Afirka amma ba tare da kowane sharadi ba gaba.

Kasar Sin kasa mai tasowa ce mafi girma a duniya, nahiyar Afirka nahiya ce mafi girma inda ake da kasashe masu tasowa. Tattalin arzikin kasar Sin da na kasashen Afirka za su iya taimakawa juna kwarai, kuma yana da makoma mai haske. Ana cike da imani cewa, dangantakar sada zumunta a sahihanci da zama tare cikin lumana da kara yin hadin guiwar moriyar juna da neman bunkasuwa tare a tsakanin Sin da kasashen Afirka za ta kara samun cigaba kamar yadda aka saba. (Sanusi Chen)