Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-01 11:25:18    
Kasar Sin za ta shimfida wata hanyar dogo ta zamani a Nijeriya

cri
A ran 1 ga wata, ma'aikatar kula da harkokin hanyar dogo ta kasar Sin ta bayar da labari cewa, kasar Sin za ta taimaki kasar Nijeriya kan ayyukan shimfida tagwayen hanyar dogo ta zamani a kasar Nijeriya domin cimma burin sabunta hanyar dogo ta kasar Nijeriya.

An bayar da labari cewa, tsawon wannan hanyar dogo ya kai kilomita 1315, saurinta zai kai kilomita 150 a kowace awa. Jimlar kudin kwagila ta kai dalar Amurka biliyan 8.3. Wadannan kudade sun hada da rancen kudin dalar Amurka biliyan 1 da bankin shigi da fici na kasar Sin ya bayar a kan kudin ruwa kadan. Babban kamfanin shimfida hanyar dogo ta kasar Sin ne yake daukar hakkin yin zane da sayen kayayyaki da aiwatar da dukkan ayyukan shimfida wannan tagwayen hanyar dogo. Wannan kwagila mafi girma ce da kamfanin kasar Sin ya samu a kasashen waje.

Shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Nijeriya ya nuna godiya ga taimakon da gwamnatin kasar Sin ta bayar. Yana ganin cewa, tabbas ne wannan aiki zai bayar da muhimmiyar gudummawa ga neman bunkasuwar tattalin arzikin kasar Nijeriya. (Sanusi Chen)