Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-01 11:01:03    
Shugabanni da kafofi watsa labarai na Afirka sun nuna yabo sosai ga dangantakar hadin kai ta aminci tsakanin Sin da Afirka

cri
Lokacin da za a kira taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ba da jimawa ba, shugabanni da kafofin watsa labarai na kasashen Afirka sun nuna yabo sosai ga dangantakar hadin kai ta aminci tsakanin Sin da Afirka.

A ran 30 ga watan Oktoba, yayin da shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ke zantawa da manema labarai na kasar Sin, ya bayyana cewa, an kafa dangantakar da ke tsakanin Afirka da Sin ne bisa tushen zaman daidai wa daida da moriyar juna da kuma nuna girmama wa juna. Kuma yana ganin cewa, ko dangantakar hadin kai ta aminci tsakanin kasashen Masar da Sin, ko dangantakar hadin kai ta aminci tsakanin Afirka ta Sin, makomarsu tana da kyau. Yana fatan za a iya ci gaba da ingantawa da raya dangantakar hadin gwiwa ta aminci tsakanin Masar da Sin da kuma tsakanin Afirka da Sin ta hanyar kokarin da bangarorin biyu suka yi tare.

A ran 31 ga wata, shugaban kasar Zambia Levy Patrick Mwanawasa ya bayyana cewa, kasar Zambia za ta yi waiwayen zumuntar da ke tsakanin Sin da Afirka ta wannan taron koli, kuma ana fatan za a ci gaba da sa kaimi ga dangantakar aminci tsakanin kasashen Zambia da Sin.

A ran 30 ga watan Oktoba, jaridar The Analyst ta kasar Liberiya ta bayar da sharhi, inda ta nuna yabo sosai ga dangantakar aminci tsakanin Sin da Liberiya. A cikin sharhin, an nuna cewa, gwamnatin kasar Liberiya da ke karkashin jagorancin shugaba Sirleaf tana dora muhimmanci sosai kan hadin gwiwa tsakaninta da kasar Sin, kuma ana sa ran cewa, kasashen biyu za su samu ra'ayi daya wajen bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu a gun taron koli.(Kande Gao)