Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-01 10:41:35    
Kafofin watsa labarai na kasar Liberiya sun nuna yabo sosai ga dangantakar aminci tsakanin kasashen Sin da Liberiya

cri
A ran 30 ga watan Oktoba, jaridar The Analyst ta kasar Liberiya ta bayar da sharhi, inda ta nuna yabo sosai ga dangantakar aminci tsakanin Sin da Liberiya.

Kuma a cikin sharhin, an nuna cewa, kasar Sin ta kiyaye dangantakar aminci tsakaninta da kasar Liberiya cikin dogon lokaci, kuma ta nuna mata juyayi kan matalolin da ta fuskanta. Yanzu kasar Sin ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya fiye da 500 zuwa kasar Liberiya, haka kuma ta sa hannu a cikin ayyuka masu yawa na kasar wajen bunkasa tattalin arziki.

Bugu da kari kuma sharhin ya bayyana cewa, shugabannin kasashen Afirka fiye da 40 za su halarci dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi a birnin Beijing ba da jimawa ba. Shugaba Johnson-Sirleaf ta kasar Liberiya shugaba ta farko ne da ta iso birnin Beijing. Gwamnatin kasar Liberiya da ke karkashin jagorancin shugaba Sirleaf tana dora muhimmanci sosai kan hadin gwiwa tsakaninta da kasar Sin, kuma ana sa ran cewa, kasashen biyu za su samu ra'ayi daya wajen bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu a gun taron koli.(Kande Gao)