Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-31 21:36:05    
Jama'ar Sin suna maraba da zuwan aminanmu na Afrika don halartar tarurruka

cri
Ran 31 ga wata, Malam Liu Jianchao, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, jama'ar kasar Sin suna jiran aminanmu na Afrika da za su zo Beijijng don halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika, 'yan birnin Beijing sun nuna goyon bayansu ga matakai da gwamnatin birnin ya dauka wajen kayyadde zirga-zirgar motoci don tabbatar da yin taron yadda ya kamata.

A gun taron manema labaru da aka saba yi a Beijing, Malam Liu Jianchao ya ce, don ba da tabbaci ga yin taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika yadda ya kamata, gwamnatin birnin Beijing ta dauki wasu matakai wajen kayyadde zirga-zirgar motoci, ta haka za a kawo tasiri ga zirga-zirgar motoci a wasu fannoni, amma daga ra'ayoyin da aka samu daga wajen 'yan birnin, an gano cewa, 'yan birnin sun nuna babban goyon bayansu ga wannan taron koli na Beijing da za a yi, kuma sun fahimci matakai da aka dauka wajen kayyadde zirga-zirgar motocin. (Halilu)