Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-31 20:08:03    
Kasar Sin ta ba da sahihin taimako ga kasashen Afirka wajen yaki da talauci

cri
Yau da shekaru 50 da suka wuce, jamhuriyar jama'ar Sin ta kulla huldar diplomasiyya tare da kasashen Afirka. A cikin shekarun nan 50 da suka wuce, kasashen Sin da Afirka sun hada gwiwarsu a wajen bunkasa tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a da bunkasa zaman al'umma da dai sauransu. Duk da kasancewarta kasa mai tasowa, amma kasar Sin ta ba da babban taimako ga kasashen Afirka. A cikin 'yan shekarun baya, tattalin arzikin kasar Sin ya yi ta bunkasa cikin sauri, kuma karfin kasar ya yi ta ingantuwa, amma duk da haka, kasar Sin ba ta manta da aminanta na Afirka ba. Don taimaka wa kasashen Afirka wajen saukaka fatara, kasar Sin ta dauki matakai da dama, ciki har da soke basussukan kasashen Afirka da kara shigowa da kayayyaki daga kasashen Afirka da aiwatar da hadin gwiwar fasaha da dai sauransu, wadanda suka kara amfana wa kasashen Afirka a hakika kuma kai tsaye. Sabo da haka, kasashen Afirka da yawa suna ganin taimakon yana da amfani, kuma sun nuna yabo da kuma maraba gare shi.

Taimakon da kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka yana da sigogi iri biyu na musamman, wato da farko dai, ta tsai da ayyukan da za ta yi bisa abubuwan da kasashen Afirka ke bukata cikin gaggawa. Na biyu kuwa, ba hade suke da ko wane sharadi na siyasa ba, wato ba a matsa wa kasashen Afirka lamba ba ta hanyar ba da taimako. Wani abin da kasashen duniya suka fi jinjina shi ne, yayin da kasashen Afirka ke fama da dimbin basussuka, a matsayinta na tsohuwar abokiyarsu wadda ita kanta ba ta da arziki, kasar Sin ta cire ko rage basussuka da yawa da kasashen Afirka suka ci. Game da batun, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Qin Gang ya ce, ta hakan, kasar Sin tana fatan za ta iya ba da hakikanin taimako ga kasashen Afirka wajen saukaka talauci da kuma bunkasa tattalin arziki. Ya ce,'kasar Sin ita kanta kasa ce mai tasowa, kuma ba ta da arziki, amma muna kokarin taimaka wa kasashen Afirka wajen yaki da talauci da tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki. A cikin 'yan shekarun baya, musamman ma bisa tsarin dandalin hadin kan Sin da Afirka, mun riga mun soke basussukan kasashen Afirka 31 wadanda suka fi fama da basussuka da kuma rashin samun ci gaba, wadanda kuma gaba daya yawansu ya kai kudin Sin yuan biliyan 10 da miliyan 500.'

A matsayinta na wata kasa mai tasowa wadda ke daukar nauyin da ke bisa wuyanta, har kullum, kasar Sin tana dukufa a kan taimakawa kasashen da ke fama da talauci, ciki har da kasashen Afirka, wajen bunkasa tattalin arzikinsu, don neman samun zaman jituwa da albarka a duk fadin duniya. Ban da wannan, a gun taron shugabanni da aka yi a watan Satumba na shekarar da ta gabata dangane da cikon shekaru 60 da kafa MDD, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya dauki alkawarin cewa,'kasar Sin ta soke harajin kwastan duka da ta buga a kan kayayyakin kasashe 39 mafiya rashin samun ci gaba wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da ita, kuma za ta kara ba da taimako ga kasashen da ke tsananin fama da basussuka da talauci da kuma kasashe mafiya rashin samun ci gaba. Nan da shekaru biyu masu zuwa kuma, kasar Sin za ta soke dukannin rancen kudi marasa ruwa ko da ruwa kadan da ya kamata kasashen da ke tsananin fama da basussuka wadanda kuma suka kulla huldar diplomasiyya da ita su biya kafin karshen shekara ta 2004, amma ba su yi ba.'

Ban da ita kanta, kasar Sin kullum tana kira ga gamayyar kasa da kasa, musamman ma kasashe masu sukuni da su dauki hakikanan matakai, su soke ko kuma rage dimbin basussukan da kasashen Afirka suka ci, don fid da kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka daga matsalolin basussuka.

Game da alkawarin kasar Sin da kuma matakan da ta dauka, jakadan kasar Nijer a kasar Sin, Adamou Boubakar ya nuna babban yabo, ya ce,'wannan matakin da kasar Sin ta dauka wani abu ne mai kyau a gare mu, don zai taimaki kasashen Afirka kamar Nijer, da su biya wannan bashi za su sa kudin cikin wani fanni na kara kyautata zaman rayuwar mutanen Nijer. To, wannan abu ne da muke godiya a kai. Muna fatan Sin za ta kara yin irin wadannan abubuwa, wanda zai taimaki kasashe kamar Nijer su sami ci gaba da bunkasuwa. Mun san mutanen Sin abokai ne na gaske, abin da suka ce za su yi za su yi, kuma za su yi ta da zuciya guda.'(Lubabatu)