A halin yanzu, Sin da Afirka sun riga sun zama muhimman abokan cinikayya ga juna, dangantakarsu ta shiga cikin wani sabon mataki, wato suna hadin kai a fannoni daban daban domin samun bunkasuwa tare da samun zamansu mai jituwa. A cikin wannan hali, ya zama tabbas ne kafa dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka.
Game da haka, Wang Hongyi ya gaya mana cewa, 'Da farko kasashen Afirka sun kaddamar da wannan dandalin tattaunawa, sa'an nan kasar Sin ta shiga cikinsa. Bayan haka, dangantakar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka ta kara samun bunkasuwa a kan siyasa da tattain arziki da dai sauran fannoni. A kan shirya wannan dandalin tattaunawa cikin lokaci da aka tsara har dandalin ya zama wani tsari, to, wannan yana da muhimmiyar ma'ana sosai, wannan tsari ya daga matsayin dangantakar bangarorin biyu a wani sabon mataki na bangarori da dama.'
Mr Wang ya bayyana cewa, dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ba ta shafi wata kasa kawai ba, ta shafi dukkan kasashen Afirka, sabo da haka ya zama tilas a kafa wani tsari da bangarori da dama suke yin shawarwari a kansa. Bisa wannan tsari, bangarorin biyu za su shirya tarurruka cikin lokacin da aka tsara, su tattauna a kan wasu manyan al'amuransu tare, kuma su yi gyara kan wasu manufofinsu, haka kuma su dauki matakai domin tinkarar wasu sababbin abubuwa da ke faruwa a kan hadin kansu. Sabo da haka, muna iya cewa, wannan tsari ya ba da taimako sosai ga bunkasuwar dangantakar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka. Ban da wannan kuma, kafuwar tsarin dandalin tattaunawa a kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka ya dace da zaman misali ga kasashen duniya, wato da farko a raya dangantaka a tsakanin bangarori biyu, sa'an nan bangarori da dama su shiga cikin shawarwarinsu, bayan haka, bangarori da dama su hada kansu a shiyya shiyya har ma su kafa kungiyar gamayyar tattalin arziki ta shiyyoyinsu. Sabo da haka ne, kafuwar dandalin tattaunawa a kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka ya zama wani abu na tabbas na saurin bunkasuwar dangantakar Sin da Afirka.
Lallai, wannan dandali ya kara sa kaimi ga bunkasuwar abokantaka da hadin ka a tsakanin Sin da Afirka a fannoni daban daban. Game da haka, Wang Hongyi ya jaddada mu'amalar da bangarorin biyu suke yi a kan al'adu. Ya ce,
'A duk duniya, ana musanyar al'adu. Idan ana son kafa wata duniya mai jituwa, to, ya kamata bangarori daban daban su kara fahimtar juna da kuma girmama al'adu daban daban.'
Wang Hongyi ya ce, a kan yi musayar al'adu a tsakanin Sin da Afirka, kafuwar cibiyoyin Confucious ta zama wani abu da ya fi jawo hankulan jama'a. A shekarar da ta wuce, kasar Sin ta riga ta kafa wata cibiyar Confucious a jami'ar Nairobi ta kasar Kenya, haka kuma za ta kafa wata daban a jami'ar Kairo ta kasar Massar. Dalilin da ya sa aka yi haka shi ne domin mutanen Afirka su kara samun ilmi a fannin al'adun kasar Sin, da kuma halin da ake ciki a kasar Sin, ta yadda za a kara zurfafa aminci a tsakaninsu. Yin mu'amala a kan al'adu ya zama wani muhimmin tushe ga dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka, haka kuma yana da wani amfani na musamman ga bunkasuwar dangantakar abokantaka da hadin kai a tsakanin Sin da Afirka.
Bayan da Wang Hongyi ya bayyana kafuwar dandalin tattaunawa a kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka da tarihin bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka, ya gaya mana cewa, yana sanya ran alheri sosai ga kyakkyawar makomar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka. Ya ce,
'A matsayin wata babbar kasa mai tasowa, kasar Sin ta zama wata aminiyar kasashen Afirka. Sabo da haka ne, kamata ya yi bangarorin biyu su taimakawa juna a kan harkoki da yawa.'
Wang Hongyi ya ci gaba da cewa, tare da saurin bunkasuwar kasar Sin da Afirka, bangarorin biyu za su kara hada kansu a fannoni daban daban, haka kuma za su mayar da dangantakarsu cikin wani sabon mataki. Kasar Sin za ta kara ba da taimako ga kasashen Afirka, kasashen Afirka su ma za su kara taka wata muhimmiyar rawa a kan bunkasuwar kasar Sin cikin dogon lokaci. Hadin kai da ke tsakanin Sin da Afirka zai ba da taimako ga shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa a duk duniya, haka kuma zai kawo moriya ga duk duniya.(Danladi)
|