Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-30 17:42:16    
Yanayi da zaman fararren hula na jihar Guangxi sun samu kyautatuwa sosai sakamakon yin amfani da iskar gas da ake samu daga taki

cri

Iskar gas da ake samu daga taki wani irin tsabtaccen makamashi ne da ake iya yin amfani da shi sosai, kuma yana iya maye gurbin man fetur da iskar gas da kuma kwal bisa wani matsayi. A 'yan kwanakin da suka gabata, yayin da wakilinmu ya kai ziyara a jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashi kansa ta kasar Sin, ya gano cewa, yanayi da zamantakewar fararren hula na wurin ya samu kyautatuwa sosai sakamakon yin amfani da iskar gas da aka samu daga taki.

Hu Decai, shugaban ofishin kula da harkokin yaki da talauci na jihar Guangxi ya gaya mana cewa, gwamnatin wurin ta riga ta shigad da batun rayawa da yin amfani da iskar gas da ake samu daga taki a cikin shirin taimaka wa manoman yankin wajen yaki da talauci da kuma samun wadata, amma yanzu ana bukatar ci gaba da bunkasa iskar gas da ake samu daga taki daga fannoni da yawa. Ya bayyana cewa, Iskar gas da ake samu daga taki tana da amfani a fannoni da dama, daya daga ciki shi ne ana iya magance matsalar makamashi da manoman yankin ke fuskanta, da rage lalata gundun daji, ta yadda za a iya kiyaye muhallin halittu yadda ya kamata. Dayan kuwa shi ne wurin samar da iskar gas da ake samu daga taki yana da tsabta a gwargwado, kuma ana iya yin amfani da kashin shanu da na dawaki don samun iskar gas, haka kuma abubuwan shara da ke cikin wurin samar da iskar za su zama nagartacen taki ne ga shuke-shuke. Ban da wannan kuma, ana iya saukaka rayuwa ga jama'a musamman ma mata bayan da aka yi amfani da iskar."

1  2  3