Tun daga ran 3 zuwa ran 5 ga watan Nuwamba, za a shirya taron koli da taron ministoci na dandalin tattaunawar hadin guiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a nan birnin Beijing. Lokacin da ake yin taron, birnin Beijing zai bai wa baki na Afirka hidimomi bisa halin musamman na kowane bako.
Shugabannin kasashen Afirka za su sauka a otel-otel masu matsayin taurari 5 guda 22 a birnin Beijing lokacin da suke halartar taron. Wadannan otel-otel suna share fagen maraba da zuwan shugabannin kasashen Afirka, kuma suna shirya hidimomi bisa halin musamman na kowanensu. Ma'aikata wadanda za su yi hidima ga shgabannin a cikin otel-otel, za su iya gaishe da wadannan shugabanni da harsunan Turanci da Faransanci har da yaren kasashensu. Sa'an nan kuma, an buga sunayen shugabanni da na matansu a kan riguna da silifofi da za su sanya lokacin da suke kwana a cikin dakin shugaba na otel-otel.
Bugu da kari kuma, wadannan otel-otel sun riga sun kebe dakunan dafa abinci ga kuku-kuku na shugabannin kasashen Afirka, kuma za su samar da abinci da abin sha iri iri ga kungiyoyin wakilan kasashen Afirka bisa bukatar da suke nema. (Sanusi Chen)
|