Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-30 10:55:02    
Shugaban Guinea-Bissau da firayin ministan Angola sun sauko kasar Sin

cri

Ran 29 ga wata da yamma, shugaban kasar Guinea-Bissau Joao Bernardo Vieira ya sauka birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, ya fara ziyarar aikinsa a kasar Sin. A wannan rana kuma, firayin ministan kasar Angola Fernando dos Santos "Nando" ya sauka birnin Shenzhen. Ya zuwa yanzu shugabannin kasashe 3 na Afirka sun sauko kasar Sin don halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Aifkra da za a bude a ran 4 ga watan Nuwamba.

A lokacin da yake ziyara a Shanghai, Mr. Vieira ya bayyana cewa, a cikin shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta sami saurin bunkasuwar tattalin arziki, ta sami babbar nasara. Kasar Guinea-Bissau tana maraba da 'yan masana'antun kasar Sin da su kara zuba jari a kasar.

Ban da wannan kuma, shugaban kasar Liberia madam Ellen Johnson-Sirleaf da ta sauko nan Beijing a ran 28 ga wata ta je birnin Shenzhen ziyara a ran 29 ga wata. Ta bayyana cewa, makasudinta na kai wa Shenzhen ziyara shi ne domin koyon fasahohi na zamani da Shenzhen ya samu wajen samun bunkasuwa, tana kuma fatan birnin Shenzhen da wani lardin kasar Liberia za su kulla huldar abokantaka a tsakaninsu, zai kuma kulla huldar abokantaka da hadin gwiwa da kasarta a fuskar tattalin arziki.(Tasallah)