Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-27 22:16:53    
Tsari na hakika, kuma hadin gwiwa na sahihi

cri

Aminai makaunatai, kuna sane da cewa, za a gudunar da taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika a Beijing da kuma zama na uku na ministocin dandalin tattaunawar nan gaba ba da jimawa ba. A cikin dogon lokacin da ya shige, kasar Sin da kasashen Afrika suna ta kyautata zaman cude-ni-in-cude-ka tsakaninsu a fannin siyasa, da tattalin arziki da cinikayya ,da kiwon lafiya, da al'adu da kuma na yalwatuwar zamantakewar al'umma da dai sauran fannoni. Hakan ya janyo zaman alheri ga jama'ar bangarorin biyu.

Mr. Xu Jinhu, shugaban sashen kula a harkokin Afrika na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin aikatawa na bangaren kasar Sin na dandalin fadi-albarkacin-baki kan harkokin cude-ni-in-cude-ka da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya bayar da wani bayani a kan jaridar " Renmin Ribao" ta kasar Sin a ran 26 ga watan da muke ciki.

Bayanin ya ce, kafa dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar tsakanin Sin da Afrika, wani muhimmmi mataki ne na muhumman tsare-tsare da kasar Sin da kasashen Afrika suka dauka domin kara dankon zumuncin gargajiya, da karfafa hadin gwiwa na sahihi, da fuskantar kalubale tare dake gabansu da kuma samun bunkasuwa a nan gaba; haka kuma, wani irin sabon gwaji ne suka yi domin ingiza hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Hakikanan ayyuka da aka yu cikin shekaru 6 da suka shige sun shaida, cewa tsarin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar tsakanin Sin da Afrika ya taka muhimmiyar rawa wajen daukaka ci gaban yunkurin cude-ni-in-cude-ka da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika daga dukkan fannoni.

Daga baya dai, bayanin ya bayyana wassu muhimman halayen musamman na wannan tsarin dandalin tattaunawa:

Halin musamman na farko, shi ne yin zaman daidaici da samun moriyar juna. Sanin kowa ne, har kullum kasar Sin da kasashen Afrika suna yin zaman daidai wa daida da nuna sahihiyar zumunta da juna. Hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika, ya kasance tamkar taimakon juna ne da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa. Har kullum bangarorin biyu suna aiwatar da wannan ka'ida;

Halin musamman na biyu, shi ne yin hadin kai na hakika. Bangarorin biyu wato kasar Sin da kasashen Afrika suna bin manufar " Daukar matakai " na samun moriyar juna da samun ci gaba tare;

Halin musamman na uku wato na karshe, shi ne yin hangen nesa kan kyakkyawar makoma. Bangarorin biyu sun fi bayar da karfi wajen yalwata kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika daga dukkan fannoni kuma cikin dogon lokaci. Sa'annan kuma suna kara kyautata tsarin dandalin tattaunawar ta hanyar shimfida demokuradiyya da bude kofa, ta yadda za su dinga samar da karfin ingizawa ga yunkurin yin kyakkyawan hadin kai tsakanin Sin da Afrika.

A cikin shekaru 6 da suka wuce, manyan jami'ai na kasar Sin da na kasashen Afrika sun kara yin mu'amala tsakaninsu, shugabanni da ministocin harkokin waje na kasar Sin da na kasahen Afrika sun kai ziyara da juna har sau 200, kuma sama da 50 daga cikinsu, shugabannin kasar Sin ne suka kai ziyara a kasashen Afrika. Musamman ma, a watan Afrilu da watan Yuni na wannan shekara, shugaba Hu Jintao da firaminista Wen Jiabao na kasar Sin suka kai ziyara daya bayan daya a wassu kasashen Afrika. Wannan dai ya tabbatar da ,cewa shugabannin kasar Sin da na kasashen Afrika suna mai da hankali sosai kan gada kuma yayata zumuncin gargajiya na kasar Sin da kasashen Afrika.

A shekarar 2000, yawan kudaden da kasar Sin da kuma kasashen Afrika suka samu daga cinikayya ya zarce dola biliyan 10; A shekarar bara ma, ya kai kusan dola biliyan 40. Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar Sin ta rigaya ta nuna gatanci wajen buga haraji ga hajoji iri 190 kirar kasar Sin, wadanda aka yi jigilarsu zuwa kasashe 30 mafi talauci na Afrika wadanda kuma suka kulla huldar diplomassiya tare da kasar Sin. Lallai kasar Sin ta sami sabon ci gaba wajen zuba jari a kasashen Nahiyar Afrika.

A karshe dai, bayanin ya hakkake, cewa taron koli na Beijing na dandalin tattauna kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika da za a gudanar da shi zai iya kara samun fahimtar juna da kuma kafa sabon yanayin kyautata kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. ( Sani Wang )