Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-26 18:32:41    
Makomar hadin guiwa tsakanin Sin da Nijeriya tana da haske

cri

Kasar Nijeriya wadda take da mutane miliyan 130, wata babbar kasa ce a yankunan yammacin Afirka. Tana taka muhimmiyar rawa kan harkokin siyasa na shiyya-shiyya. Kasar Sin ta dade tana mai da hankali kan dangantakar da ke tsakaninta da kasar Nijeriya. Kwanan baya, wakilinmu Bello Wang wanda yake zaune a kasar Nijeriya ya gana da jakadan kasar Sin Xu Jianguo da ke kasar Nijeriya. Yanzu ga rahoton da malam Bello ya aiko mana daga Nijeriya.

Jakada Xu ya ce, a shekarar 1971 ce aka kafa dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Nijeriya. Bayan kafuwar wannan dangantaka, dangantakar siyasa da ke tsakaninsu ma tana ta samun cigaba mai dorewa. Mr. Xu ya ce, "Tun daga lokacin kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, dangantakar da ke tsakaninsu tana ta samun cigaba mai dorewa. Musamman a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, manyan jami'an kasashen biyu suna ta kai wa juna ziyara a kullum. Manyan jami'ai, musamman shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Nijeriya su kan nuna kyakkyawan halin zuciya ga kasar Sin, kuma suna sada zumunta tsakanin Sin da kasar Nijeriya."

Mr. Xu ya ce, kasashen Sin da Nijeriya dukkansu kasashe masu tasowa ne da ke da mutane mai tarin yawa. Yanzu dukkansu suna da nauyin raya tattalin arziki da aka dora musu, kuma suna da kwatankwancin ra'ayi daya kan batutuwa masu yawa na kasa da kasa da yawa. Mr. Xu ya ce,

"Alal misali, kan batun yadda za a kiyaye hakkin bil Adam, da farko dai, dole ne mu tabbatar da ikon neman kasancewa a duniya da na neman bunkasuwa da ikon fama da talauci da kuma na raya tattalin arziki da dai makamantansu. A kan wadannan fannoni, muna da kwatankwancin ra'ayi daya. Sa'an nan kuma, kasashen biyu suna amincewa juna kan harkokin siyasa a kullum. Sakamakon haka, dangantakar da ke tsakaninsu tana samun cigaba yadda ya kamata."

Bugu da kari kuma, Mr. Xu yana ganin cewa, yayin da kasashen biyu suke amincewa juna kan harkokin siyasa, suna kuma kara yin hadin guiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya. A shekarar bara kawai, yawan kudaden cinikayya da aka yi tsakanin kasashen Sin da Nijeriya ya kai dolar Amurka biliyan 3. Yanzu, kasar Nijeriya tana matsayi na biyu a Afirka wato a bayan kasar Afirka ta kudu kawai wajen shigar da kayayyakin kasar Sin. A waje daya kuma, masana'antun kasar Sin da dama sun riga sun shiga kasar Nijeriya, kuma suna yin hadin guiwa da bangaren kasar Nijeriya a fannoni iri iri ciki har da ayyukan yau da kullum. Mr. Xu ya kara da cewa, "Wasu masana'antun kasar Sin sun riga sun shiga kasuwar kasar Nijeriya. Alal misali, kamfanin CGCOC ya dade yana haka rijiyoyi a kasar Nijeriya, kuma ya riga ya samu amincewa daga gwamnati da jama'ar kasar Nijeriya. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, masana'antu da kamfanoni na kasar Sin suna shiga kasar Nijeriya sannu a hankali. Ya zuwa yanzu, yawan kudaden kwangilolin da suka samu ya riga ya kai dalar Amurka kimanin biliyan 3."

Yayin da kasashen Sin da Nijeriya suke kara yin hadin guiwa a fannonin siyasa da tattalin arziki, suna kuma kara mai da hankali wajen yin hadin guiwa a fannoni ilmi da al'adu da kimiyya da fasaha. A fannin kimiyya da fasaha, kamfanin Babbar Ganuwa na kasar Sin ya sayar wa kasar Nijeriya wani tauraron dan Adam irin na sadarwa mai samfurin Dongfanghong 4. Wannan ne karo na farko da kamfanin Babbar Ganuwa ta kasar Sin ya fitar da wani cikakken tauraron dan Adam baki daya. A watan Maris na shekara mai zuwa, za a harba wannan tauraron dan Adam. Mr. Xu ya ce, "Wannan ne karo na farko da jama'ar Afirka, ko jama'ar Nijeriya, ko jama'ar bakakken fata da za su mallaki wani cikakken tauraron dan Adam nasu. Ba ma kawai wannan tauraron dan Adam na sadarwa zai kyautata halin sadarwa da watsa shirye-shiryen rediyo da ake ciki a kasar Nijeriya ba, har ma zai bayar da muhimmiyar gudummawa kan yadda za a kyautata halin sadarwa da watsa shirye-shirye da ake ciki a yankunan da ke kudu da hamadan Sahara."

Bugu da kari kuma, wasu jami'o'i 4 na kasar Nijeriya suna yin mu'ammala da ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Nijeeriya domin suna fatan za a iya kafa sashen koyar da Sinanci a wadannan jami'o'i.

Mr. Xu ya ce, makomar raya dangantaka a tsakanin Sin da Nijeriya tana da haske sosai. Ko shakka babu, kasashen biyu za su kara samun cigaban hadin guiwa a fannonin siyasa da tattalin arziki da cinikayya da kimiyya da fasaha da al'adu da kuma ilmi. (Sanusi Chen)