Ran 25 ga wata, matasa 14 masu sa kai na lardin Hebei na kasar Sin sun tafi kasar Habasha don yin aikin sa kai a kasar har na tsawon shekara daya.
Bisa labarin da muka samu, an ce, an zabi wandannan matasa 14 daga masu sa kai faye da dubu daya, kuma sun zo daga hukumomin ilmi, da kiwon lafiya, da aikin gona, kuma su gwanaye ne a fannoninsu. A lokacin da suke kasar Habasha, za su tafiyar da aikin sa kai a fannonin koyar da Sinnanci, aikin ba da agaji, koyar da fasahohin aikin gona, da ilmin injunan kwakwalwa.
Kafin masu sa kai su tafi su nuna cewa, za su yi kokari don ba da gudummawa ga bunkasuwar huldar abokantaka da ke tsakanin jama'an kasashen biyu.
|