Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-25 17:53:44    
Taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka tana da muhimmiyar ma'ana

cri

A kwanan nan, yayin da ministan harkokin waje na kasar Kenya Mr. Tuju da ministan cinikayya na kasar Uganda Mr. Jhunjhunwala da kuma ministan shari'a na kasar Algeria Mr. Blaise ke zantawa da manema labarai na kasar Sin, sun bayyana cewa, makomar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka tana da kyau sosa, kuma taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi ba da dadewa ba zai ba da mihimmin tasiri wajen ci gaba da inganta hadin gwiwa tsakaninsu.

Mr. Tuju ya bayyana cewa, taron koli na Beijing wani matukar muhimmin taro ne, ba kawai ya samar da dama wajen karfafa dangantakar siyasa da diplomasiyya tsakanin Sin da Afirka ba, har ma ta samar da wata dama wajen inganta cinikayya tsakanin Sin da Afirka da kuma hadin gwiwa tsakaninsu daga dukkan fannoni. Sabo da haka kasar Kenya ta mai da hankali sosai kan taron.

Mr. Jhunjhunwala ya yi imani cewa, za a ci gaba da kiyaye da kuma inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Uganda da Sin da kuma tsakanin Afirka da Sin a fannin tattalin arziki da cinikayya sakamakon kira taron. Haka kuma za a sa kaimi ga raya huldar da ke tsakanin kasashen Uganda da Sin daga dukkan fannoni ta taron.

A nasa bangare, Mr. Blaise yana ganin cewa, muhimmin amfanin da kasar Sin ke bayarwa lokacin da take sa hannu a ciki al'amuran duniya da kuma bunkasuwar tattalin arzikinta za su taimaka wa kasashen Afirka wajen farfado da tattalin arzikinsu. Haka kuma za su kafa tushe wajen ci gaba da karfafa hadin gwiwar aminci tsakanin Sin da Afirka daga dukkan fannoni don moriyar juna.(Kande Gao)