Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-25 17:03:57    
Taron koli na Beijing zai ciyar da hadin gwiwar aminci da ke tsakanin Sin da Afirka gaba daga dukan fannoni

cri

A farkon watan Nuwamba mai zuwa, a nan birnin Beijing, za a yi taron koli na Beijing, wato taron ministoci na karo na uku na dandalin hadin kan Sin da Afirka, wanda kuma zai kasance taro mafi kasaita a tarihin harkokin diplomasiyya na sabuwar kasar Sin wanda ke da tsawon shekaru 57. Kwanan baya, jakadan kasar Sin a Kenya, Zhang Ming ya yi hira da wakilinmu, yanzu sai ku sha rahoton da wakilinmu ya aiko mana dangane da hirar da suka yi.

Mr.Zhang ya ce, tun bayan da aka kafa dandalin hadin kan Sin da Afirka a watan Oktoba na shekara ta 2000, dandalin ya taka muhimmiyar rawa a wajen bunkasa huldar aminci da hadin kai a tsakaninsu. A cikin shekaru shida da suka wuce, hakikanan abubuwa sun tabbatar da cewa, dandalin ya riga ya zama wani muhimmin dandali na yin shawarwari tsakanin kasashen Sin da Afirka da kuma wani tsari mai amfani wajen aiwatar da hadin gwiwa a tsakaninsu. Shekarar da muke ciki shekara ce ta cikon shekaru 50 da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin sabuwar kasar Sin da kasashen Afirka, don neman inganta zumuncin gargajiya da kuma hadin gwiwar aminci a tsakaninsu, bangarorin biyu sun tsai da cewa, za su mayar da taron ministoci na karo na uku na dandalin hadin kan Sin da Afirka a matsayin wani taron koli na shugabanni. Jakada Zhang ya ce,"bisa jigon 'sada zumunta da zaman lafiya da hadin gwiwa da ci gaba', shugabannin Sin da Afirka za su waiwayi nasarorin da kasashen Sin da Afirka suka samu a hadin gwiwar aminci da ke tsakaninsu a cikin shekaru 50 da suka wuce da kuma a wajen dandalin hadin kan Sin da Afirka a cikin shekaru 6 da suka wuce, kuma za su tattauna yadda za su bunkasa sabuwar huldar abokantaka irin ta zaman daidaici a fannin siyasa da samun nasarori tare a hadin gwiwar tattalin arziki da kuma koyi da juna a fannin al'adu, kuma za su tsara makomar hadin gwiwarsu a nan gaba, ban da wannan, za su yi musanyar ra'ayoyi a tsakaninsu a kan wasu manyan al'amuran duniya.'

Mr.Zhang ya kuma yi imani da cewa, bisa kokarin da bangarorin biyu suke yi tare, tabbas ne taron zai kasance wani kasaitaccen taro mai hadin kai, kuma zai kasance wani muhimmin al'amari a tarihin huldar da ke tsakanin Sin da Afirka. Ya ce,'ina imani da cewa, wannan taron da za a yi zai taimaka wajen kara fahimtar juna da dankon zumunci a tsakanin Sin da Afirka, kuma zai kara ciyar da hadin gwiwar aminci da ke tsakanin Sin da Afirka gaba daga dukan fannoni, haka kuma zai taimaka wajen inganta hadin kai da hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma inganta zaman lafiya da bunkasuwar duniya.'

Yayin da ya tabo magana a kan manufar kasar Sin a kan Afirka, Jakada Zhang ya ce, taron koli na Beijing da za a yi, taro ne mafi kasaita a tarihin harkokin diplomasiyya na sabuwar kasar Sin wanda ke da tsawon shekaru 57, kuma zai shaida cewa, inganta huldar aminci da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, wani muhimmin kashi ne na huldar diplomasiyya da ke tsakanin kasar Sin da kasashen waje. Ya ce,'bana shekara ce ta cikon shekaru 50 da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin sabuwar kasar Sin da kasashen Afirka. A cikin shekarun 50 da suka wuce, an sami manyan sauye-sauye a halin da duniya ke ciki da kuma halin da kasashen Sin da Afirka ke ciki, amma duk da haka, tushen hadin gwiwar Sin da Afirka bai sauya ba, kuma yanayin sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka ma bai sauya ba. Bangarorin biyu na Sin da Afirka dukansu suna kishin kara bunkasa zumuncin gargajiya da ke tsakaninsu da inganta hadin gwiwar zaman daidaici da samun moriyar juna a tsakaninsu, don neman samun bunkasuwa tare. Har kullum, gwamnatin kasar Sin da shugabanninta suna dora muhimmanci sosai a kan kasashen Afirka da kuma huldar da ke tsakaninsu da Sin, kuma suna mayar da bunkasa huldar aminci da hadin gwiwa ta gargajiya a tsakaninsu a wani muhimmin matsayi na harkokin diplomasiyya na kasar Sin.'(Lubabatu)