A yayin da kasashen Sin da Massar suke gamu da manyan bala'i ko wahaloli, bangarorin biyu su kan nuna tausayi ga juna, kuma su kan taimakawa juna. Bayan da aka aikata farmakin ta'addanci sau biyu a Shamm Sheikh da Dahab na kasar Massar, nan da nan shugaban kasar Sin Hu Jintao ya buga wayar jejeto ga takwaransa Mr Mubarak, kuma ya bayyana cewa, kasar Sin tana son kara hadin kai da kasashen duniya ciki har da kasar Massar domin ci gaba da yaki da ta'addanci da kiyaye zaman lafiyar duniya. Bayan da wani hadarin mota da ke daukar 'yan yawon shakatawa na Hongkong na kasar Sin ya faru a kasar Massar, shugaban kasar Massar Mr Mubarak ya mai da hankali sosai a kan batun, shi kansa ya ba da umurni ga hukumomin da abin ya shafa da su daidaita wannan batu yadda ya kamata.
Kasar Sin tana mai da hankali sosai a kan amfanin kasar Massar a harkokin shiyya shiyya da na duniya, har kullum kasar Sin tana mayar da kasar Massar a matsayin muhimmiyar abokiyar hadin kai a duniyar Larabawa da Afirka. A watan Janairu na shekarar 2004, shugaba Hu na kasar Sin ya kai ziyara a kasar Massar, inda suka bayyana kafuwar dandanlin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Larabawa. Amfanin da kasar Massar ta bayar a harkokin Afirka yana kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka.
A fannonin tattalin arziki da cinikayya, kasashen Sin da Massar suna iya taimakawa juna sosai, kuma hadin kansu yana da babban boyayyen karfi ga yin hadin gwiwar tattalin arziki. Bangarorin biyu suna hadin kansu a fannonin sana'o'in kire kire da aikin gona da sake sake da likitanci da kare muhalli da dai sauransu lami lafiya. Bisa kididdigar gwamnati da aka bayar, an ce, a shekarar 2005, yawan kudaden da suka samu wajen yin cinikayya ya kai kudin Amurka dala biliyan 2 da miliyan 145, wanda ya karu da kashi 36.1 cikin dari bisa na makamancin lokaci. A halin yanzu, yawan ayyukan da kasar Sin ta zuba jari a kasar Massar ya kai 186, yawan kudinsu ya kai kudin Amurka dala miliyan 220.
1 2
|