Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-23 21:31:47    
Hadin gwiwa da ke tsakanin Sin da Afirka ya zama wani abin koyi, a cewar shugaban kasar Comoros

cri

Yayin da shugaban kasar Comoros Mohamed Sambi ke zantawa da manema labarai na kasar Sin a kwanan nan, ya bayyana cewa, kasar Sin tana nuna goyon baya ga kasashen Afirka wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma samar da taimakon kayayyaki da kudade masu yawa ga kasashen Afirka, sabo da haka hadin gwiwa da ke tsakanin Sin da Afirka ya zama wani abin koyi.

Kuma shugaba Sambi ya nuna yabo ga kasar Sin da ta inganta dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka. Ya yi farin ciki da kuma nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin da jama'ar Sin da suka gayyace shi domin halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka.

Ban da wannan kuma ya bayyana cewa, yanzu bunkasuwar duk duniya bai daya tana bayar da muhimmin tasiri ga harkokin siyasa da tattalin arziki na duk duniya, kira taron a daidai wannan lokaci zai samar da dama wajen inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afirka ya bayyana ra'ayin kasar Sin wajen sa kaimi ga zumunci da hadin gwiwa tsakaninta da Afirka, haka kuma ya bayyana cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan cika alkawarin da ta yi wajen samun zaman lafiya da tsaron kai da kuma bunkasuwa. Yawancin kasashen Afirka za su aika da wakilansu domin halartar taron koli na Beijing da kuma yin ziyara tsakanin manyan jami'an kasashen Sin da Afirka, wannan kuwa ya nuna cewa, ana raya dangantakar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da kyau sosai.(Kande Gao)