Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-23 18:41:34    
Hanyoyin da kasar Sin ta shimfida a Afirka hanyoyi ne ta sada zumunta

cri
Hanyar dogo ta Tazara da gwamnati da jama'ar kasar Sin suka ba da taimako su shimfida a tsakanin kasashen Tanzania da Zambia a shekaru 1970 ta yi kama da gadar sada zumunta a tsakanin jama'ar Sin da Afirka. A cikin shekaru 30 da suka wuce, an kara gina gadojin sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, zumuncin da ke tsakanin bangarorin 2 sun shiga sabon mataki.

Kafin shekaru 30 da suka wuce, a cikin usur din na jirgin kasa ne, aka kaddamar da hanyar dogo ta Tazara mai tsawon kilomita 1860.5, wadda gwamnatin kasar Sin ta ba da taimakon fasaha da injuna da ma'aikata da kuma rancen kudi ba tare da biyan kudin ruwa ba, ta kuma yi shekaru 6 tana aikin shimfida ta daga birnin Dares Salaam, babban birnin kasar Tanzania zuwa sabon Kapirimposhi na lardin Katikati na kasar Zambia. Hanyar dogo ta Tazara ta goyi bayan ayyukan neman 'yancin kan al'umma a kasashen Kudancin Afirka, a sa'i daya kuma, ta ba da gudummawa wajen raya tattalin arzikin al'umma na kasashen Afirka da yawa, wadanda suka hada da Tanzania da Zambia.

Lokacin da yake zantawa da manema labaru, babban injiniya na bangaren Tanzania mai kula da aikin shimfida hanyar dogo ta Tazara Robert Mona ya bayyana cewa,'Bayan da aka kaddamar da wannan hanyar dogo, an kafa masana'antu da yawa a gefunanta, kamar su masana'antun samar da takarda da siminti, sa'an nan kuma an samu kananan kauyuka da yawa, biranen da ke gefunanta sun sami bunkasuwa. Shi ya sa hanyar dogo ta Tazara ta raya tattalin arzikin kasashen Tanzania da Zambia sosai, ta kuma daga matsayin zaman rayuwar jama'ar da ke zama a gefunanta.'

Wasu masanan kasashen yamma su ma sun amince da cewa, hanyar dogo ta Tazara tana da muhimmanci sosai ga kasashen Gabashin Afirka masu fama da talauci da su yi kokarin fitar da kansu daga talauci.

Don shimfidawa da kuma kiyaye hanyar dogo ta Tazara, kasar Sin ta taba tura ma'aikata masu fasaha 50,000. Sun yi aiki tukuru a kasashen ketare, har ma wasu 60 ko fiye sun rasu. Game da wannan kuma, darektan sashen zirga-zirga na hukumar kula da hanyar dogo ta Tazara Abdurahmani Saidi ya ce,'Abokan kasar Sin sun sa hannu cikin shimfida da kuma kiyaye wannan hanya, a cikin shekarun nan da suka wuce, sun san matsalolin da suka fuskanta sosai, saboda haka sun ba da taimako yadda ya kamata. Sinawa sun yi ta taimake su.'

Bayan da aka shimfida hanyar dogo ta Tazara, kasar Sin ta kara ba da taimako a kasashen Afirka. Suna sa hannu cikin dakin wasa na kasar Tanzania da kuma tsarin sadarwa da ya shafi kasashen Kenya da Zimbabwe da Nijeriya da sauran ayyuka. Suna yin aiki tukuru wajen raya tattalin arzikin kasashen Afirka, suna kuma gina sabbin gadojin sada zumunta a tsakanin jama'ar Sin da Afirka.

A wata mai zuwa, za a kaddamar da hanyar mota ta Kipsigak-Serem-Shamakhokho mai tsawon kilomita 53 a kasar Kenya, wadda gwamnatin kasar Sin ta ba da kudi, kamfanin Wuyi na kasar Sin ta ba da taimako wajen shimfida. An shimfida wannan hanya a wurin da ya yi suna ne saboda samar da ganyen shayi. Kaddamar da ita zai nuna muhimmiyar ma'ana ga kasar Kenya wajen fitar da shayi, da kuma aiwatar da shirin neman ci gaba da Kungiyar Hada Kan Tattalin Arzikin Kasashen Gabashin Afrika ta tsara.

Darektan sashen kula da ayyukan kasar Kenya na kamfanin Wuyi na kasar Sin Wan Dongsheng ya bayyana cewa, Ma'aikatar kula da ayyukan gine-gine na kasar Kenya ta nuna babban yabo kan ingancin wannan hanyar mota da lokacin aiki da kuma hadin gwiwar da ke tsakanin kamfaninsu da hukumar wuri, a galibi dai sun nuna gamsu sosai.'

Mun yi imanin cewa, saboda shimfida hanyoyin da ke kawo wa mazaunan wurin alheri, jama'ar Sin da Afirka za su rika raya dangantakar abokantaka ta gargajiya da ke tsakaninsu.(Tasallah)