Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-22 18:27:12    
Kasashen Angola da Sin sun hada kansu bisa zaman daidai wa daida da moriyar juna

cri
Yayin da mataimakin ministan kudi na kasar Angola Eduardo de Morais ke zantawa da manema labaru na kasar Sin a kwanan nan, ya bayyana cewa, kasar Sin tana takawa muhimmiyar rawa a cikin ayyukan sake gina kasar Angola, kuma kasashen Angola da Sin sun hada kansu ne bisa tushen zaman daidai wa daida da girmama wa juna da kuma moriyar juna.

Haka kuma Mr. Morais ya nuna cewa, bayan da aka kawo karshen yakin basasa na kasar Angola a shekara ta 2002 wanda aka yinsa shekara da shekaru, ayyukan sake gina kasar sun samu ci gaba sosai bisa taimakon da kasashen duniya ciki har da kasar Sin suka bayar. Yarjeniyoyi masu yawa wajen ba da rancen kudi da gwamnatocin kasashen Sin da Angola suka daddale a jere sun samar da kudade da fasahohi ga kasar Angola, kuma sun ba da taimako sosai kan ayyukan sake gina kasar.

Ban da wannan kuma Mr. Morais ya bayyana cewa, yana fatan za a inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ta taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin kai tsakanin Sin da Afirka da za a yi a ba da dadewa ba.(Kande Gao)