Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-20 17:06:07    
Kasashen Sin da Tunisia sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar hadin gwiwa kan kimiyya da fasaha

cri
A ran 19 ga wata, a kasa Tunisia, kasashen Sin da Tunisia sun rattaba hannu a kan 'yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin da Jamhuriyar kasar Tunisia wajen kimiyya da fasaha'.

Wakilin ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Wu Zhongze da Taieb Hadhri, ministan nazarin kimiyya da fasaha na kasar Tunisia sun sa hannu a kan yarjejeniyar a madadin gwamnatocin kasashen biyu.

Bisa abubuwan da aka tanada a cikin yarjejeniyar, an ce, bangarorin biyu za su inganta hadin gwiwarsu a fannin kimiyya da fasaha bisa tushen zaman daidai wa daida da moriyar juna. Ban da wannan kuma bangarorin biyu za su goyi baya da kuma karfafa kwarin gwiwar hukumomin nazarin kimiyya da kuma kungiyoyin da ke nuna sha'awar nazarin kimiyya da fasaha na kasashen biyu da su hada kai tsakaninsu. Bugu da kari kuma bangarorin biyu za su kafa wani kwamitin hadin gwiwar kimiyya da fasaha, da kuma kira taro sau daya a ko wadannen shekaru biyu domin tattauna da kuma zartas da ayyukan hadin gwiwa tsakaninsu.(Kande Gao)