Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-20 09:37:23    
Sabon ci gaban birni mai suna Jingdezhen na kasar Sin wanda ya shahara wajen yin tangaram

cri

A shekarun baya, masana'antun yin tangaram guda biyar na birnin Jingdezhen sun hada kansu gu daya, sun kafa wani babban kamfanin yin tangaram na masu hannun jari na birnin, sun fara yin tangaram masu kyau na zaman yau da kullum, kuma sun fara yin bincike kan tsara fasalin tangaram da zane-zanensu da sauransu. Da malam Yu Guoqing, magajin gari na Jingdezhen ya tabo magana a kan shahararren samfurin tangaram da ake kirkirowa a birninsa, sai ya ce, "daga abubuwa da suka faru, an gano cewa, masana'antu suna samun taimako daga wajen shahararren samfurin kayayyakinsu don kara daga matsayinsu kan takarar da ake yi a kasuwanni. Haka nan kuma tarin masaya ma suna cin gajiyarsu wajen kare moriyarsu."

Ban da wannan kuma idan an so a yi ta samun ci gaba wajen raya wannan birni, hedkwatar tangaram, to, wajibi ne, a horar da kwararru masu dimbin yawa. Malam Liu Yuanchang, masanin ilmin zane-zane na kasar Sin ya bayyana ra'ayinsa a kan wannan cewa, "idan akwai kwararru, to, akwai makoma mai kyau. Kwararru jari ne. Yanzu a lokacin da muke gudanar da harkokin masana'antu ta hanyar fasahar zamani, to, wajibi ne, a bar kwararru su yi kokarin yin amfani da fasaha wajen kirkiro sabbin abubuwa, ta yadda za a mayar da birnin Jingdezhen, ya zama wani birnin yin tangaram na zamani."

Yanzu, an riga an kafa wata jami'ar koyon aikin tangaram a birnin Jingdezhen, yawan malaman koyarwarta da dalibanta ya kai kimanin dubu 10. A nan ne ake ta horar da kwararru a fannin aikin tangaram domin masana'antun yin tangaram na wurare daban daban na kasar Sin. Masana'antun yin tangaram na birnin nan ma su kan iya daukar dalibai da suka gama karatu daga jami'ar nan don bunkasa harkokinsu. Mun tabbatar da cewa, masana'antun yin tangaram na birnin Jingdezhen suna da makoma mai kyau sosai.(Halilu)


1  2  3