Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-19 16:40:27    
Taron koli na Beijing na FOCAC ta zama tamkar wata sabuwar ishara ce ta dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka

cri
A ran 18 ga wata, yayin da James Michel, shugaban kasar Seychelles ke ganawa da Geng Wenbing, jakadan kasar Sin da ke Seychelles a fadarsa, ya bayyana cewa, taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wanda za a yi nan ba da dadewa ba zai zama tamkar wata sabuwar ishara ce ta dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka.

Kuma shugaba Michel yana ganin cewa, kira taron koli na Beijing ya nuna cewa, kasar Sin wadda ta samu bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri, da kuma kara bayar da muhimmin tasiri a duniya tana dora muhimmanci kan dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka, kuma ta dauki kasashen Afirka tamkar abokanta da ke da matsayin daidai wa daida.

Ban da wannan kuma shugaba Michel ya bayyana cewa, ya yi farin jiki sosai da takwaransa na kasar Sin Hu Jintao ya aika masa gayyata, kuma zai shugabanci tawagar wakilai ta kasar don halatar taron da kuma kawo wa kasar Sin ziyarar aiki. Yana jiran yin musanyar ra'ayoyinsa tare da Shugaba Hu Jintao da sauran shugabannin kasar Sin kan ci gaba da raya dangantakar hadin gwiwa ta aminci tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni.(Kande Gao)