Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-16 21:42:00    
Hadin gwiwar da ke tsakanin Zimbabuwe da Sin yana amfana wa bangarorin biyu baki daya, in ji ministan harkokin wajen Zimbabuwe

cri

A ranar 16 ga wata a birnin Harare, babban birnin kasar Zimbabuwe, ministan harkokin waje na kasar, Mr.Simbarashe Mumbengewi ya bayyana cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin Zimbabuwe da Sin yana amfana wa bangarorin biyu baki daya, kuma shi kyakkyawan misali ne a wajen bunkasa huldar da ke tsakanin kasashe masu tasowa, amma ba wai 'sabon mulkin mallaka' ba ne a cewar wasu kafofin yada labarai na yammacin duniya.

A lokacin kusantowar taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, Mr. Simbarashe Mumbengewi ya yi hira da wakilin gidan rediyonmu, inda ya musanta furucin da wasu kafofin yada labarai na yammaci suka yi na cewa, wai hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka 'sabon mulkin mallaka' ne da kasar Sin ta bullo da shi a Afirka. ya ce, kasashen yammacin duniya sun san mene ne mulkin mallaka, amma ba su san huldar da ke tsakanin kasashe masu tasowa ba, kuma ba su da wata fahimta dangane da huldar da ke tsakanin Zimbabuwe da Sin da kuma huldar da ke tsakanin Afirka da Sin. Wasu kasashen yammaci ba su son ganin bunkasuwar kasar Sin a Afirka.

Mr.Mumbengewi ya kuma kara da cewa, yana fatan taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka zai kara inganta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka a fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma harkokin duniya.(Lubabatu)