Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-13 17:35:34    
Neman samun moriyar juna da ci nasara tare aihinin abu ne na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, in ji shugaban Ghana

cri
Lokacin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin a birnin Accra, babban birnin kasar Ghana a kwanan baya, shugaban kasar Ghana Mr. John Kufuor, wanda zai halarci taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi ba da dadewa ba, ya bayyana cewa, yana fatan kasar Sin da kasashen Afirka za su yi tattaunawa cikin sakin jiki kan warware batutuwan da suka shafi ciniki da fitar da fasaha da zuba jari da dai sauransu, ta yadda za su dasa harsashi yadda ya kamata wajen samun moriyar juna da cin nasara tare.

A cikin intabiyun musamman na tsawon mintoci 30 da aka yi masa, Mr. Kufuor ya yi amfani da kalmomi 2 wato 'moriyar juna' da 'cin nasara tare' har sau 5 wajen jaddada muhimmin abu na hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Ya bayyana cewa, dimbin shugabannin kasashen Afirka za su taru a Beijing, za su tattauna tare da shugabannin kasar Sin kan damar da ba su taba yin amfani da ita ba wajen yin hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2, wannan yana muhimmiyar ma'ana.

Mr. Kufuor ya kara da cewa, kasar Sin tana zama wata kasa mai karfi a fannin tattalin arziki a duk duniya, kasashen Afirka kuma suna neman samun abokan yin hadin gwiwa don raya kansu. A cikin irin wannan hali ne, kasar Sin da kasashen Afirka suna hada kansu da sauki. Kasashen Afirka suna da albarkatu mai yawan gaske, amma a baya baya ne suke. Bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ta kawo wa kasashen Afirka damar da ba su taba samunta ba wajen samun ci gaba. Shi ya sa shugabannin kasashen Afirka su kan zo kasar Sin don neman yin hadin gwiwa, har ma 'yan kasuwa na kasar Ghana fararen hula sun kara zuwa kasar Sin don sayen kayayyaki.

Kasar Ghana da ke yammacin Afirka tana mallakar dimbin albarkatun ma'addinai, ita kuma shaharariyyar shiyya ce da ke samar da koko a duniya. Shugaba Kufuor ya ce, a gun ziyarar da zai kai wa kasar Sin, yana fatan zai yi shawarwari da gwamnatin kasar Sin kan yin hadin gwiwa a fannonin aikin ma'addinai da yin amfani da ruwa wajen samar da lantarki da aikin noma, kasashen Ghana da Sin za su zuba wa juna jari kan shirye-shirye da yawa.

Har zuwa wata Maris na wannan shekara, masana'antu masu jarin kasar Sin suna gudanar da ayyuka fiye da 230 a kasar Ghana, wadanda suka shafi kera kayayyaki da aikin ba da hidima da yawon shakatawa da ciniki da gine-gine. Mr. Kufuor ya yi bayani kan wadannan ayyuka cewa, yana dora muhimmanci kan wadannan ayyuka, saboda masana'antun kasar Sin sun iya kammala ayyuka yadda ya kamata kafin lokaci ya cika, sun ba da gudummuwa wajen bunkasuwar kasashen Ghana da Burkina Faso da sauran kasashe kamar irinsu, sun kawo wa jama'ar Afirka alheri.

Game da ra'ayi na wai kasar Sin tana gudanar da sabon salon mulkin mallaka a kasashen Afirka da wasu mutane suka yi surutun banza a kai a kwanan baya, Mr. Kufuor ya ce, hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ya kawo wa kasashen Afirka fasaha da kudi da suke matukar bukata, ya kuma kawo wa jama'ar Afirka damar samun aikin yi. Ganin irin wadannan alherin da kasar Sin take kawowa, wa zai mayar da hadin gwiwa don moriyar juna da ke tsakanin Sin da Afirka tamkar ra'ayin mulkin mallaka?

Mr. Kufour ya taba kai wa kasar Sin ziyara a shekarar 2002, a lokacin nan, manyan gine-gine da kwazon mutanen kasar Sin sun burge shi sosai. A karshen wannan intabiyu na musamman, Mr. Kufour ya bayyana cewa, abin bakin ciki shi ne mai yiwuwa ne ba shi da lokacin hutu a gun ziyarar da zai kai wa kasar Sin, amma zai yi amfani da wannan dama zai yi tattaunawa da shugabannin kasar Sin yadda ya kamata, don neman daga matsayin hadin gwiwa don moriyar juna da ke tsakanin kasashen 2 zuwa wani sabon mataki.(Tasallah)