Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-12 20:18:29    
Taron koli na Beijing wani gagarumin taro ne ga dangantaka tsakanin Sin da Afirka

cri
Yayin da Mr. Jouini, shugaban tawagar kasar Tunisia ta dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka kuma ministan raya kasa da hadin kan kasa da kasa na Tunisia ke zantawa da wakilinmu a kwanan nan, ya bayyana cewa, taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wani gagarumin taro ne ga dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka, yana da muhimmiyar ma'ana. Kuma taron zai ba da taimako wajen ci gaba da bunkasa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka daga dukkan fannoni.

Kuma Mr. Jouini ya bayyana cewa, an kira wannan taro ne yayin da kasashen Afirka masu yawa suka samu ci gaba a fannin tattalin arziki da kuma kara bude kofa ga kasashen waje, wannan zai ba da taimako wajen inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin. Ban da wannan kuma ya nuna cewa, kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar da ke tsakaninta da Afirka, kuma tana ba da muhimmin tasiri a fannin karfafa hadin gwiwa tare da Afirka. Kuma yana fatan za a iya kulla huldar hadin gwiwa tsakanin Afirka da Sin daga dukkan fannoni, ta yadda za a ingiza hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a fannonin kimiyya da fasaha da al'adu da wasannin motsa jiki.(Kande Gao)