Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-11 16:52:11    
Ya kamata Afirka su yi amfani da damar da aka kai su domin cigaban dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka, a cewar Gaye

cri
A kwanan baya, an wallafi wani littafi mai suna "Sin da Afirka: Dragon da Jimina" da Adama Gaye, sanannen dan jarida na kasar Senegal ya rubuta game da dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka a kasar Faransa da yankunan Afirka. A cikin wannan littafi, marubucin yana ganin cewa, ya kamata kasashen Afirka su sake duba sabuwar dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da Afirka, kuma su fuskanci dama da kalubalen da ke gabansu domin cigaban dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka domin hanzarta saurin bunkasuwar Afirka.

Mr. Gaye ya taba kawo wa kasar Sin ziyara har sau biyu bisa gayyatar da kungiyar kasar Sin wadda ke sada zumunta a tsakanin jama'ar Sin da ta kasashen waje. Sabo da haka, ya samu sabbin kayayyaki da yawa da yake bukata domin rubuta wannan littafi. A cikin littafinsa, Mr. Gaye ya bayyana tarihin cigaban kasar Sin filla filla da dangantakar da ke tsakanin kasar Senegal da kasar Sin kuma da tarihin cigaba da halin da ake ciki game da dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka. Ya kuma yi hangen nesa kan wannan dangantaka. (Sanusi Chen)